Yadda Malamar Jami’a Ta Koma Tallan Dankali Saboda Yajin Aikin ASUU

Yadda Malamar Jami’a Ta Koma Tallan Dankali Saboda Yajin Aikin ASUU

  • Har yanzu yajin aikin malaman jami'a da aka fara tun a watan Fabrairun shekarar nan ya ki ci ya ki cinyewa
  • Daliban Najeriya da malaman jami'a sun koma neman sana'ar hannu kasancewar sun gaji da zama haka babu abun yi
  • Wata lakcara a jami'ar Uyo, Christiana Chundung Pam, ta fara tallan dankalin turawa domin dauke lalurar gabanta

Wata lakcara a jami’ar Uyo mai suna Christiana Chundung Pam ta fara sana’ar siyar da dankalin turawa domin samun tudun dafawa.

Pam wacce ta kasance mataimakiyar lakcara da aka dauka aiki a shekarar bara ta ce za ta ci gaba da wannan sana’a tata har zuwa shekaru biyar masu zuwa idan har wannan shine sadaukarwar da za ta yiwa tsarin ilimi na kasar don ya daidaita.

Kara karanta wannan

Karuwa Ta Sharbe Farjin Takwararta Da Reza Bayan Fada Ya Kaure Tsakaninsu Kan Kwastoma, Ta Shiga Hannu

Da take zantawa da wakilin jaridar Independent wanda ya gano ta tana kasa dankalinta a kasuwar Akpan Andem da ke Uyo, jihar Akwa Ibom, Pam ta ce ta kama sana’ar ne don ta kula da kanta.

Christiana
Yadda Malamar Jami’a Ta Koma Kasa Dankali A Kasuwa Saboda Yajin Aikin ASUU Hoto: Independent
Asali: Facebook

Miss Pam wacce ke siyar da kayanta a kasuwa da cikin gari, ta yi bayanin cewa ta shafe yan watanni na yajin aikin wajen taya iyayenta da suka yi ritaya aikin gona da nufin komawa aiki ba da jimawa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai sabanin tunaninta, yajin aikin ya ci gaba har bayan da suka girbe shukan nasu kuma ga tarin basussuka ciki harda kudin gidan da take haya a garin da take aiki.

Pam ta ce:

“Na yanke shawarar fara harkar siyar da dankali don na samawa kaina abun rufin asiri. Na fara aiki kenan ko shekara ban yi ba kuma ban tara abun da zai isheni koda komawa Jos ba, kasancewar na dan tsaya da wasu watanni don a janye yajin aikin.

Kara karanta wannan

Bidiyon Rahama Sadau Tana Zuba Yaren Indiyanci, Za Ta Fito A Shirin Bollywood

“Don haka da zan koma, sai da na ranci kudi a wajen wani don b azan iya daukar dawainiyar kaina da biyan kudade ba. Sai da na ranci kudi don sabonta hayar gidana na wasu watanni shida don gudun kada ya kubce mun. wannan kudin zai kare a watan Oktoba, saboda haka dole na samu wani abun yi don sabonta shi.”

Matashiyar lakcarar haifarfiyar jihar Plateau ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta nemi hanyar kawo karshen wannan yaji da kungiyar ASUU ke yi a kasar.

Ta ce tana shiga damuwa da yawan daliban da ke kiranta a kullun don jin yadda ake ciki game da yajin aikin da ke gudana da kuma muradinsu na son komawa makaranta don cimma mafarkinsu a rayuwa.

Ta yi gargadin cewa barin Baraka a tsakanin harkokin ilimi yana da illa a bangaren dalibai da malamai domin za su bukaci lokaci kafin kwakwalwarsu ta dawo daidai wajen daukar darasi.

Kara karanta wannan

Bana Wasa Da Jin Dadin Iyalina Ko Kadan Kuma Ina Shirin Rufe Kofa Da ta Hudu, Lakcara mai yara 18

Sai dai kuma, ta jaddada alwashin da ta sha cewa:

“Idan har siyar da dankali na tsawon shekaru biyar masu zuwa zai sa daliban Najeriya su samu tsarin karatu mai inganci sannan ya karfafawa lakcarori gwiwar daura damara wajen gyara goben masu zuwa a gaba, toh zan yi hakan da hannu bibbiyu.”

Gwamna El-Rufai ya rantse zai sallami duk Malaman Jami’a da ke yajin-aikin ASUU

A wani labarin, gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi barazanar korar malaman jami’ar KASU da suka shiga yajin-aikin da kungiyar ASUU ta ke yi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Malam Nasir El-Rufai yana cewa zai kori malaman jami’an jihar Kaduna da suka yi watsi da aikinsu, suka tafi yajin-aiki.

Tun watan Fubrairun shekarar nan kungiyar ASUU ta malaman jami’a take yajin-aiki a kasa, Malaman na zargin gwamnati da kin cika alkawuranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel