Wata sabuwa: Ma'aikatan wutar lantarki sun bi sahu, za su taya ASUU zanga-zanga

Wata sabuwa: Ma'aikatan wutar lantarki sun bi sahu, za su taya ASUU zanga-zanga

  • Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki sun yi shirin zanga-zangar nuna goyon baya ga kungiyar malaman jami'o'i (ASUU)
  • Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi kira ga dukkan ma'aikata su fito domin nuna kin amincewa da ci gaban yajin aikin ASUU
  • Kungiyar ASUU ta shafe watanni sama da hudu suna yajin aiki saboda wasu bukatu da ta gabatarwa gwamnatin tarayya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Punch ta ruwaito cewa, ma’aikatan wutar lantarki a karkashin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE), sun ce za su bi sahun kungiyar kwadago ta Najeriya NLC a zanga-zangar hadin gwiwa da ta shirya yi kan yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

Kungiyar kwadago ta NLC ta umarci ma’aikata da su fito zanga-zanga a fadin kasar nan a ranakun 26 da 27 ga watan Yuli domin nuna goyon bayansu ga yajin aikin da ASUU ta shiga.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

Ma'aikatan jiragen sama, ma'aikatan inshora da ma'aikatan kudi, da sauransu su ma sun yi alkawarin shiga zanga-zangar, rahoton TheCable.

Ma'aikatan wutar lantarki za su fito zanga-zanga
Wata sabuwa: Ma'aikatan wutar lantarki sun bi sahu, za su taya ASUU zanga-zanga | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Joe Ajaero, babban sakataren kungiyar NUEE, a wata wasika mai dauke da kwanan wata 22 ga watan Yuli, ya umurci dukkan mambobin kungiyar da su shiga zanga-zangar saboda dadewar da aka yi manyan makarantu a garkame.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasikar ta ce:

"A bisa umarnin NLC da kuma matsayinmu, wanda aka bayyana a babban taron kwamitin gudanarwa da majalisar zartarwa ta kasa, an umurci dukkan mambobin kungiyar da su tashi tsaye tare da taka rawar gani wajen gudanar da zanga-zangar hadin kai ra NLC/ASUU don nuna rashin amincewa da ci gaba da rufe manyan makarantun kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 26/27 ga Yuli, 2022."

Biyo bayan shawarar da kungiyar ta yanke, Najeriya na iya sake ganin wani sabon cikowa da cikar hanyoyi da zai fara a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

A makon da ya gabata, wutar lantarki ta kasar ta ruguje - a karo na bakwai kenan a cikin 2022 - wanda ya shafi kasuwanci da rayuwar al'umma da dama.

Yajin aiki: Ma'aikatan jiragen sama zasu rufe filayen jirage don taya ASUU nuna fushi

A wani labarin, kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen sama ta Najeriya (ANAP), ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen yajin aikin da ASUU ta shiga yi ko kuma za su rufe bangaren sufurin jiragen sama tare da hada kai da malaman jami’o’in.

A wata sanarwa da babban sakataren kungiyar ANAP, Kwamared Abdulrasaq Saidu ya fitar, ya bukaci shugaban kasa Mohammadu Buhari da ya kawo karshen yajin aikin ba tare da bata lokaci ba, rahoton Leadership.

ANAP ta lura cewa ci gaba da zama a gida da daliban manyan makarantu ke yi na kara haifar da munanan dabi’u a kasar nan yayin da dalibai ke yin wasu abubuwa marasa kyau da ke iya lalata makomarsu.

Kara karanta wannan

Kun cika taurin kai: Gwamnatin Buhari ta caccaki ASUU, ta ce su suka aje dalibai a gida

Asali: Legit.ng

Online view pixel