‘Yan Najeriya miliyan uku za su rasa sana'a idan Buhari ya hana yanka jakuna a Najeriya - inji dillalan jakuna

‘Yan Najeriya miliyan uku za su rasa sana'a idan Buhari ya hana yanka jakuna a Najeriya - inji dillalan jakuna

  • Kungiyar dillalan jakuna sun yi korafi ga manufar gwamnatin Buhari na kokarin haramta yanka jakuna a Najeriya
  • Najeriya na daga cikin kasashen da ke yanka jakuna domin amfani da fatarsu wajen kasuwancin kasashen waje
  • Maganar haramta yanka jakuna a Najeriya saboda wasu dalilai na hango karewar dabbobin a kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Wani batu mai daukar hankali ya fito daga kungiyar dillalan jakuna (DDA) a ranar Litinin 25 ga watan Yulin wannan shekarar

Kungiyar ta koka ga yadda majalisar kasar nan ke kokarin kawo dokar haramta yanka jakuna, lamarin da a cewar kungiyar zai haifar da zaman banza.

A cewar kungiyar sama da ayyuka miliyan uku za a rasa idan aka aiwatar da shirin haramta yanka jakuna a kasar nan, 21st Centaury Chronicle ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Banza ta faɗi: Bokaye sun damfari ɗan siyasa N24m bayan yaje neman sa'ar cin zaɓe, EFCC tayi ram da su

Shugaban kungiyar na kasa Mista Ifeanyi D*ke ne ya bayyana hakan a wajen wani taron kwana daya na jin koken jama’a da aka kan kudirori takwas na fannin noma a ranar Litinin.

Kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin noma da raya karkara wanda Sen. Bima Enagi ke jagoranta ne ya shirya taron jin ra'ayin jama'a.

Majalisa na duba yiwuwar haramta yanka jakuna
‘Yan Najeriya miliyan uku za su rasa sana'a idan Buhari ya hana yanka jakuna a Najeriya - inji dillalan jakuna | Hoto: punchng.com

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kudirin mai taken: “Kudurin tabbatar da dokar yankan jaki da fitar da kaya, 2020” ya samu daukar nauyin Sanata Yahaya Abdullahi ne a farfajiyar majalisa.

Kudirin dokan wanda ya tsallake karatu na biyu a ranar 6 ga Yuli, 2021 yana da nufin rage kashe jakuna saboda duba da dabi'u, muhalli, ilimi, tarihi, nishadi da kima ga al'umma.

Haka kuma kudurin na neman ayyana jakuna a matsayin wani nau'in dabbar da ke cikin hatsarin gaske wanda sakamakon yanka ta ba gaira ba dalili da nufin amfani da fatar jikinsu, ka iya jawo karewar dabbobin a kasa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari zai shilla Liberia don taya su murnar shekaru 175 da samun 'yanci

Mista Ifeanyi, ya ce dokar hana yankan jakuna kai tsaye ba ita ce mafita ba wajen dakile bacewar jakuna a kasar.

Ifeanyi ya ce harkallar jakuna, samar dasu da kiwonsu zai samar da miliyoyin guraben ayyukan yi kama daga makiyaya jakuna, ‘yan kasuwa, mahautan jakuna, kayan aikin sarrafa su da kuma fitar da su zuwa kasashen waje.

A cewarsa, maimakon a hana sana’ar jakuna kai tsaye, kamata ya yi gwamnati ta samar da wani tsari na hana fasa-kwaurinsu.

Ya kuma yi tsokaci da cewa:

"Shanu da muke yanka sama da 50,000 a kullum a matsayin nama ba su kare ba, to ta yaya jaki mai lokacin kiwo irin na saniya zai kare. Ya kamata mu karfafa haihuwarsu da kiwonsu.”

Wani dan majalisar wakilai, Mohammed Datti, a farkon jawabinsa, ya ce kudurin dokar na neman haramta kisa da fitar da jakuna zuwa China ne, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gidauniyar Bashir Ahmad Ta Dauki Nauyin Karatun Yarinya Mai Baiwar Lissafi Tun Daga Firamare Har Zuwa Jami’a

Gwamnatin Buhari na duba yuwuwar haramta Okada a Najeriya

A wani labarin, gwamnatin tarayya na duba yiwuwar haramta amfani da babura wanda aka fi sani da Okada a fadin kasar, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, ne ya yi tsokacin yayin da yake jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan taron majalisar tsaro ta kasa wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja.

Malami ya ce bincike ya nuna cewa amfani da babura wajen gudanar da ayyukan hakar ma’adinai a fadin kasar nan kuma sanya haramcin na iya katse hanyoyin samun kudaden yan ta’adda da yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel