Karfin hali: An kama 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangar kungiyar kwadago da ASUU

Karfin hali: An kama 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangar kungiyar kwadago da ASUU

  • Yayin da kungiyar ASUU ta malaman jami'a da NLC ta kwadago suka fito zanga-zanga, an samu dan karamin tashin-tashina
  • Rahoton da muka samo ya ce, an kama wasu 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangan, lamarin da ya tada hankali
  • Malaman jami'a sun shafe watanni suna yajin aiki, lamarin da ya kai ga shigar NLC domin jawo hankalin gwamnati

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jami’an tsaro sun damke tawagar 'yan sa kai na bogi yayin zanga-zangar da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta shirya tare da hadin gwiwar kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ke yajin aikin a Legas ranar Talata.

'Yan sa kan da aka kama da suka hada da direba da sauran 'yan tawagar sun haifar da wani yanayi na rikici bayan kama wani mai laifi.

Yadda jami;an tsaro suka kama jami'an bogi a filin zanga-zangar ASUU
Da dumi-dumi: An kama jami'an bogi a wurin zanga-zangar kungiyar kwadago da ASUU | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta leka wurin da lamarin ya faru, inda ta ga wasu ‘yan kungiyar sun shiga tsakani a halin da ake ciki amma abin ya haifar da zazzafar cece-kuce.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Hotunan NLC yayin da suka fito zanga-zangar kara ga ASUU

Sai dai an samu sauki yayin da jami'an tsaron da aka dasa domin kula da zanga-zangar suka shiga lamarin nan take.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kama 'yan sa kan na bogi kana aka mika su ga ofishin 'yan sanda. Sai dai ‘yan sandan sun ki yin magana a kai har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Dole za mu shiga lamarin nan: Ganduje ya koka kan ci gaba da yajin aikin ASUU

A wani labarin na daban, gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, a ranar Talata, ya tabbatar wa kungiyar kwadago ta Najeriya cewa kungiyar gwamnonin Najeriya za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an sasanta rikicin da ke tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i.

Ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar kwadago ta Najeriya a jihar, wadanda suka je gidan gwamnati, inda suka yi zanga-zangar nuna goyon bayansu ga ASUU, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ma'aikatan wutar lantarki za su mamaye Najeriya domin taya ASUU zanga-zangar nuna fushi

Gwamnan wanda ya koka da rikicin da aka dade ana yi ya ce, kungiyar gwamnoni za ta gana da Gwamnatin Tarayya ta fannin shawarwari domin warware rikicin da nufin ceto tsarin ilimin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel