Muhimmancin Ziyarar Shugaba Buhari Kasar Liberia - Garba Shehu

Muhimmancin Ziyarar Shugaba Buhari Kasar Liberia - Garba Shehu

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Laberiya a gobe Talata 26 ga watan Yuli dan taya kasar murnar cika shekaru 175 da samun 'yancin kai
  • Ana sa ran Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi akan muhimmancin gudanar da zabe mai kyau
  • Najeriya da Laberiya za su tattauna batutuwan da suka shafi ta'addanci akan iyakokin kasashen biyu, da kuma karfafa huldar tsaro da kasuwanci

Abuja - Fadar shugaban kasa a ranar Litnin ta sanar da cewa Shugaba Buhari zai tafi kasar Laberiya halartan bikin murnar ranar yancin kasar ta 175.

Buhari zai tafi Laberiya ne biyo bayan barazanar yan bindiga masu garkuwa da mutane inda suka fara kai hare-hare cikin birnin tarayya Abuja.

Yan Najeriya sun yi Alla-wadai da tafiye-tafiyen Buhari yayinda ake zub-da-jinin yan Najeriya a kudu da Arewa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari ya Sauka Daga mulki, ko a Tsige shi Inji Jam’iyyar NNPP

Malam Garba Shehu,Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya bayyana muhimmancin ziyarar Shugaba Buhari kasar Liberia a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Shafin sa na Facebook a Abuja.

Buhari
Muhimmacin Ziyarar Shugaba Buhari Kasar Liberia - Garba Shehu FOTO Legit.NG
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Garba ya ce ziyarar Buhari Laberiya na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta fara samun zaman lafiya na siyasa bayan fama da juyin mulki da ta yi na tsawon lokaci.

"Laberiya, Sierra -Leone tare da Najeriya za su gudanar da zabe a shekarar 2023 mai zuwa kuma ana sa ran shugaba Buhari zai yi jawabi akan muhimmancin gudanar da zabe mai kyau.
"Zaman lafiya da tsaro a Laberiya da Sierra Leon na da mahimmanci ga Najeriya musamman idan aka yi la'akari da dimbin arzikin da Najeriya ta kashe wajen tabbatar da tsaro a kasashe biyun.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari zai shilla Liberia don taya su murnar shekaru 175 da samun 'yanci

"Inda ba dan Najeriya ke shugabancin ECOWAS ba da yanzu ba waɗannan kasashe biyun, da ba a sami Laberiya a kan taswira ba a halin yanzu.

Bangaren kasa da kasa, Najeriya da Laberiya za su tattauna batutuwan da suka shafi ta'addanci a kan iyakokin kasashen biyu, da karfafa huldar tsaro da kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel