Malamin addini: APC ba za ta je ko ina ba a 2023 tun da Tinubu ya zabi Musulmi abokin gami

Malamin addini: APC ba za ta je ko ina ba a 2023 tun da Tinubu ya zabi Musulmi abokin gami

  • Wani fitaccen malamin addinin kirista ya fito ya yi bayani, ya ce babu inda APC za ta je a zaben 2023 mai zuwa
  • Ya bayyana haka ne a martaninsa na yadda jam'iyyar APC ta ba da tikitin takarar shugaban kasa da mataimaki ga musulmai
  • Tun farkon watan nan aka ta samun cece-kuce daga kiristocin Najeriya kan batun tikitin musulmi da musulmi na APC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kwara - Wani malami mai tsanain tsaurin kishin addinin Kirista Rt. Rabaran Olusola Akanbi, a karshen mako ya ce mabiya addinin kirista a kasar nan ba za su goyi bayan tikitin musulmi da musulmi na jam’iyyar APC a zabe mai zuwa ba.

A cewarsa, irin wannan matakin ya sabawa hadin kai, zaman lafiya da ci gaban al’ummar kasar nan, rahoton jaridar This Day.

Kara karanta wannan

2023: Sanusi II ya yi Jawabi a Game da Zabe, ya Bayyana cikas 1 da ake Fuskanta

Fasto ya ce APC ba za ta ci zabe ba a 2023
Malamin addini: APC ba za ta je ko ina ba a 2023 tun Tinubu ya zabio Musulmi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Da yake jawabi a wajen taron 2022 karo na 2 na SYNOD na Diocese a Offa a jihar Kwara, Akanbi ya bayyana cewa, lamarin na jam’iyyar APC mai mulki ba zai kai jam’iyyar a ko’ina ba a fagen zabe a tsarin lissafin siyasa.

A wajen taron wanda dan takarar Sanatan Kwara ta Kudu a zaben 2023, Sanata Rafiu Adebayo Ibrahim ya halarta, Akanbi ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina so in yi kira ga mabiya addinin Kirista da su tashi tsaye don karbar katunan PVC dinsu don gudanar da aikin 'yan kasa a zabe mai zuwa."

Ya ce tattara katunan zaben su na dindindin zai kuma taimaka musu wajen zaben shugabanni masu nagarta da za su samar da zaman lafiya da daidaiton addini a fagen siyasar kasa.

Malamin ya kuma yi kira da hakuri a zaman lafiya a tsakanin ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da bambancin addini da kabilanci ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

Akanbi ya koka da kalubale daban-daban na zamantakewa da tattalin arziki da siyasa da kasar ke fuskanta da suka hada da rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arzikin kasa, da rashin kula da fannin ilimi.

Don haka ya yaba wa Sanata Ibrahim bisa yadda yake da kyakkyawar alaka da malamai da kuma al’ummar Kirista, tare da yi masa addu’ar samun nasara.

Tun da farko, Ibrahim, wanda ya kasance bako a wurin taron ya yaba wa mabiya addinin Kirista kan yadda suke karfafa hadin kan addini da zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar, inda ya ce hakan ya kuma kara dankon zumunci a tsakanin Musulmi da Kirista a jihar.

2023: Ku kwantar da hankali, za fa ku ci zaben nan, Buhari ga Tinubu da Shettima

A wani labarin, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi batu mai ban dariya a fadarsa da ke Abuja yayin da yake martani ga zabo Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na zaben 2023.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

Shugaba Buhari, cikin barkwanci ya ba Tinubu da Shettima kwarin gwiwar lashe zaben shugaban kasa da ke tafe a shekara mai zuwa, Leadership ta ruwaito.

Buhari wanda ya karbi bakuncin dan takarar mataimakin shugaban kasa jim kadan bayan shugabannin APC da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun kaddamar dashi, ya ce ya yi matukar farin ciki da zabo tsohon gwamnan na jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel