Shugaba Buhari Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar FRSC Na Riƙo

Shugaba Buhari Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar FRSC Na Riƙo

  • Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗa Dauda Biu mukaddashin shugaban dakarun hukumar FRSC ta ƙasa
  • Biyo bayan ritayar Corps Marshal Bobiye Oyeyemi, Buhari ya naɗa babban mataimakinsa ta fannin kudi
  • A ranar Litinin, 25 ga watan Yuli, Oyeyemi ya miƙa harkokin tafiyar da hukumar ga sabon Corps Marshal na riko

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin Mista Dauda Biu, a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa FRSC biyo bayan ritayar Boboye Oyeyemi.

Mista Oyeyemi ne ya sanar da haka yayin miƙa al'amuran jami'an hukumar ga Biu a hedkwatar FRSC da ke birnin tarayya Abuja ranar Litinin.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin hukumar FRSC, ACM Bisi Kazeem, ya fitar yau Litinin a Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Atiku, Tinubu sun gamu da cikas a kokarin gaje Buhari, wasu ɗaruruwan mambobin PDP da APC sun sauya sheƙa

Dauda Biu.
Shugaba Buhari Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar FRSC Na Riƙo Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Oyeyemi ya bayyana cewa naɗin Mista Biu a matsayin sabon muƙaddashin Corps Marshal ya fara aiki ne daga ranar 24 ga watan Yuli, 2022 kuma yana masa fatan nasara a zangon mulkinsa bayan kama aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban majalisar FRSC, Malam Bukhari Bello, ya taya Dauda Biu murna bisa naɗin da aka masa kuma ya roke shi da ya ɗora daga inda ya tsaya kuma ya nuna ya dace da kujerar.

Bello ya ƙara da cewa tsohon Corps Marshal ya gina kyakkyawan tubali ga jami'an hukumar, bisa haka ya roki Biu ya ɗora daga inda ya tsaya.

Waye sabon shugaban dakarun FRSC?

Dauda Biu ya gode wa majalisar jagororin FRSC da fadar shugaban ƙasa bisa naɗa shi wannan muƙamin kuma ya sha alwashin ba zai ba su kunya ba.

Kafin zuwansa wannan muƙamin, Biu ya kasance mataimakin Corps Marshal ta ɓangaren kuɗi da tattali a Hedkwatar hukumar FRSC.

Kara karanta wannan

Daga kwanciya bacci, Ɗan shugabar Kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya ya rasu

Ya fara aiki a hukumr ne a shekarar 1988 kuma ya yi aiki mai kyau a tsawon wannan lokacin a kowane wuri ya tsinci kansa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Biu ya kammala karatun digirinsa na biyu a fannin tafiyar da kasuwanci daga jami'ar ABU Zariya kuma ya rike ƙaramin mataimakin Corps Marshal ta fannin kuɗi da tattali a 2014 kafin zama babban mataimakin a 2016.

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya aike da muhimmin sako ga shugaban APC yayin da ya cika shekara 79

A sakon ta ya murnan karin shekara, Buhari ya yaba wa tsohon gwamnan bisa gudummuwar da ya bayar a tarihin Najeriya.

Sanata Abdullahi Adamu, ya cika shekara 79 a duniya, manyan jiga-jigan siyasa musamman na APC sun taya shi murna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel