Bayan Kuje, ‘Yan ta’adda na Tsara Yadda za su Shiga Wasu Kurkuku 3 a Jihohin Arewa
- ‘Yan ta’adda suna kitsa yadda za su sake aukawa wasu gidajen yari da ke Arewacin kasar nan
- Za a iya kai hari domin fitar da ‘yan ta’ddan da ke tsare a kurkukun Zamfara, Gusau da Katsina
- Jami’an tsaro sun samu labarin wannan ta’adi, sun sanar da hukumar da ke kula da kurkuku
Nigeria - Wani rahoto na musamman da ya fito daga Premium Times ya bayyana ‘yan ta’adda su na tsara yadda za su aukawa wasu gidajen gyaran hali.
Rahoton da aka fitar a ranar Litinin, 25 ga watan Yuli, 2022 ya nuna jami’an tsaro sun fahimci ana niyyar fara fasa kurkukun garin Gusau, jihar Zamfara ne.
Bayan nan kuma bayanan sirrin da jami’an tsaro suka samu ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda suna neman shiga gidajen yarin da ke Birnin Kebbi da Katsina.
Jaridar ta ce burin ‘yan ta’addan shi ne su kubutar da wasu mayakansu da yanzu haka suke tsare.
Tuni har an aikawa hukumar kula da gidajen gyaran hali na kasa watau NCS da wannan rahoto na bayanan sirri da aka samu domin su dauki mataki.
Jami’an tsaro sun fahimci ‘yan ta’ddan za su kai hare-haren ne daki-daki domin ba su da karfin da za su fasa duka gidajen yari a jihohi uku a lokaci guda.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ana harin karshen mako
Bayanan da ke hannun jami’an tsaro sun nuna ‘yan bindigan za su iya aukawa gidan yarin Gusau a ranar Juma’a mai zuwa watau 29 ga watan Yuli 2022 kenan.
Tunanin ‘yan bindigan shi ne zuwa wannan lokaci, manyan jami’an da ke tsare da gidan kurkukun sun je hutun karshen mako, ko kuma ba su a wajen aikinsu.
Sannan a lokacin ne za a fi jin dadin shiga da wayoyin salula cikin kurkuku da taimakon gandurobobi.
‘Yan ta’adda za su boye a unguwanni
Jami’an tsaro sun fahimci wadanda ke niyyar wannan aiki za su boye ne a yankunan Ungwan Gwaza (Zamfara) da Kofar Soro (Katsina), suna jiran lokaci.
A Kebbi kuwa, ‘yan ta’addan za su tare ne a Kwaido a karamar hukumar Augie, su boye cikin jama’a tun kafin ranar da suke sa ran za su aukawa kurkukun.
An fasa kurkukun Kuje
Mayakan Boko Haram, Ansaru, da ISWAP daga Arewa maso gabas, sun shiga wasu yankin. Ana da labarin ISWAP da Ansaru ne suka shiga kurkuku na Kuje.
Wannan karo, miyagun suna so su kai wadannan hare-hare ne a jihohin Arewa maso yamma. Yankin na fama da ta’addacin miyagun ‘yan bindiga da Boko Haram.
Asali: Legit.ng