Ban Ni Na Nemi A Bani Sarauta Ba, In Ji Shugaban Yan Bindiga Da Aka Nada Sarki a Zamfara
- Ado Aleiro, shugaban yan bindiga wanda aka nada sarautan Sarkin Fulani a masarautan Yandoton Daji ya ce ba shi ya nemi sarautar ba
- Aleiro ya ce sabon sarkin Yandoto ne ya masa tayin sarautar kuma da farko bai yarda ba amma bayan tattaunawa da manya sai ya amince
- Dan bindigan ya kuma ce ba shi da hannu a mummunan harin da aka kai a kauyen Kadisau a Katsina inda aka kashe a kalla mutane 100
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Hatsabibin dan bindiga, Ado Aleiro, wanda a baya-bayan nan aka nada shi Sarkin Fulani a masarautar Yantodo a Jihar Zamfara, ya ce ba shi ya bukaci a nadi shi sarauta ba, rahoton Daily Trust.
Dan bindigan, wanda ake zargi da addabar wasu yankunan arewa maso yamma, ne ya bayyana hakan cikin wata hira da DW Hausa ta yi da shi.
Ya ce, "Wannan sarauta ni tsakani da Allah ban neme ta ba, nema na aka yi a kanta kuma da farko ban yarda ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Bayan tattaunawa da shugabannin kan lamarin, suka nuna cewa bai kamata in bada masa kasa a ido ba tunda shi sabon sarki ya ce ga abin da ya ke so a masarautarsa; haka yasa na amince."
Aleiro ya kuma musanta cewa shine ya kitsa kashe fiye da mutane 100 a kauyen Kadisau a karamar hukumar Faskari ta Jihar Katsina.
Ya ce bai san wadanda suka kai harin ba, ya kara da cewa, "Don Allah ka tafi ka tambayi dagacin Kadisau; ramuwar gayya ce, ba hannu na; kawai an saka ni ciki ne."
Da labari ya bayyana cewa an nada shi sarki, mutane da yawa sun nuna kin amincewarsu amma aka yi nadin sarautan awanni bayan masarautar ta sanar da dage nadin.
An yanke shawarar ba shi sarautar ne saboda rawar da ya taka wurin sulhu tsakanin masarautar da yan bindiga da ke adabar karamar hukumar Tsafe a jihar.
Gwamna Bello Matawalle ya saka doka ta hana sarakuna nadin sarauta ba tare da samun amincewa daga gwamnatin jiha ba.
Dan Bindigan Da Aka Nada Sarauta a Zamfara, Aleru, Ya Kashe Mutane 100 A Katsina, In Ji Rundunar Yan Sanda
A gefe guda, Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da cewa shugaban yan bindiga, Ado Aleru, wanda aka nada sarauta ranar Alhamis da ta gabata a masarautar Yandoto Daji a Zamfara, har yanzu suna nemansa ruwa a jallo.
Rundunar yan sandan ta ce ana zargin Alero da kashe mutane 100 mazauna Jihar Katsina, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Kakakin rundunar, Gambo Isah, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke martani kan nadin sarautar da aka yi wa shugaban yan bindigan a Zamfara.
Asali: Legit.ng