Yan Bindiga Sun Sace Mai Tallar Burodi, Sun Bukaci N500,000 Matsayin Kudin Fansa
- Yan bindiga da suka sace wani mai sayar da burodi a unguwar Ifawara a Osun sun nemi a biya N500,000 don fansarsa
- Wani mazaunin garin Wale Babatude ya tabbatar da sace mai tallar burodin ya ce da farko N5m aka nema amma aka rage zuwa N500,000
- Mutanen unguwar sun fara karo-karo domin hado kudin da za a ceto shi yayin da rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Osun - Wasu masu garkuwa da mutane a Osun sun bukaci a biya su N500,000 a matsayin kudin fansar wani mai sayar da burodi da suka sace a safiyar Litinin.
Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace mai sayar da burodin da aka fi sani da 'get in' a Ifawara yayin da ya ke raba burodi da motarsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda bincike ta nuna, an sace wanda abin ya faru da shi ne misalin karfe 4 na asubahi a express road da ke Iwaraja a jihar, rahoton Vanguard.
Masu garkuwar, daga bisani sun aike da sako ga mutanen unguwar suna neman a biya su Naira miliyan 5 kafin a sako shi.
Sai dai, wani mazaunin Ifewara, Wale Babatude ya shaidawa Vanguard cewa an rage kudin fansar zuwa N500,000 kuma mutanen unguwa sun fara karo-karo domin ganin an sako wanda aka sacen.
Kalamansa:
"Da gaske ne, an sace 'get in' jiya, an tsinci motarsa da hajarsa, wato burodi, a titi kuma daga baya mun samu sako na neman biyan fansa ta Naira miliyan 5.
"Sai dai, daga bisani an rage kudin zuwa Naira 500,000 kuma mun fara yin karo-karo don tara kudin da za a sako shi."
Martanin Rundunar Yan sanda kan lamarin
Rundunar yan sandan Jihar Osun ta bakin mai magana da yawunta, Yemisi Opalola, ta tabbatar da afkuwar lamarin.
Zamfara: Za A Fara Rataye Yan Bindiga Da Masu Garkuwa Da Mutane
A gefe guda, Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka ta yaki da yan bindiga da laifuka masu alaka a jihar, rahoton Daily Nigerian.
A karkashin dokar, wacce ta fara aiki nan take, ta tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk dan bindiga da laifuka masa alaka da hakan a Zamfara.
Da ya ke jawabi jim kadan bayan rattaba hannu kan dokar, Matawalle ya ce dokar na cikin matakai ne na yaki da yan bindiga, masu garkuwa da satar shanu a Zamfara.
Asali: Legit.ng