Yan bindiga sun yi garkuwa da limaman Katolika 2 a Kaduna
- Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da wasu limaman darikar Katolika guda biyu a ranar Juma'a
- Maharan sun sace Rev. Fr. John Mark Cheitnum da Rev. Fr. Donatus Cleopas, a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna, yayin da suke hanyar zuwa wani aiki
- Kansilan darikar Katolika a Kafancha, Rev. Fr. Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya tabbatar da faruwa lamarin inda ya nemi a taya su da addu'a
Kaduna - Rahotanni sun kawo cewa tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da Limaman darikar Katolika guda biyu, Rev. Fr. John Mark Cheitnum da Rev. Fr. Donatus Cleopas, a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.
Chietnum ya kasance shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya a karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna, jaridar The Nation ta rahoto.
Da yake tabbatar da lamarin, Kansilan darikar Katolika a Kafancha, Rev. Fr. Emmanuel Uchechukwu Okolo a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli, ya ce miyagun sun yi awon gaba da limaman ne a ranar Juma’a, Channels TV ta rahoto.
Okolo ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Cike da radadi muke sanar maku da labarin sace limamanmu biyu, Rev. Frs. John Mark Cheitnum da Donatus Cleopas.
“Mummunan al’amarin na garkuwa da su ya wakana ne da misalin karfe 5.45 na yammacin ranar 15 ga watan Yuli bayan da limaman biyu ke a hanyarsu na sauke nauyin da ke kansu a karamar hukumar Lere da ke jihar Kaduna.
"Muna rokon a taya mu da addu'a don a sako su cikin gaggawa da lafiya, muna kuma fatan yin kira ga jama’a da su guji daukar doka a hannunsu.
"Za mu yi amfani da duk hanyoyin da suka dace don tabbatar da sakin su cikin sauri da aminci."
Yan Bindiga Sun Kashe Dan Uwan Tsohon Gwamna Adamu Mu'azu, Sun Kuma Sace Iyalansa
A wani labarin kuma, mun ji cewa an bindige wani Mu'azu Danladi, dan shekara 25, dan uwan tsohon gwamna Ahmad Adamu Mu'azu a kauyen Boto na karamar hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi.
An kashe Danladi ne a lokacin da yan bindigan suka kutsa gidan iyalan Mu'azu a safiyar ranar Laraba.
An sace mutane uku yayin harin da ya bawa mutanen kauyen mamaki.
Asali: Legit.ng