Buhari Ga Yan Najeriya: Idan Da Kun San Wahalar Da Ake Sha A Wasu Kasashe Da Kun Gode Wa Allah

Buhari Ga Yan Najeriya: Idan Da Kun San Wahalar Da Ake Sha A Wasu Kasashe Da Kun Gode Wa Allah

  • Shugaba Buhari ya ce mutanen kasar za su rika gode wa Allah a halin da suke ciki da sun san wahalar da wasu kasashen Afirka ke ciki
  • Shugaban na Najeriya ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyarar ban girma a fadar Sarkin Katsina, Dr Abdulmumini Kabir Usman a Jihar Katsina
  • Buhari ya bukaci yan Najeriya su cigaba da hakuri a yayin da gwamnati ke iya kokarinta domin tabbatar da cewa suna rayuwa cikin walwala da zaman lafiya

Daura, Katsina - Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yan Najeriya za su gode wa Allah idan da sun san wahalar da wasu kasashen Afirka ke sha a yanzu, rahoton Daily Trust.

Buhari ya furta hakan ne yayin da ya kai wa Sarkin Katsina, Dr Abdulmumini Kabir Usman ziyarar ban girma a fadarsa a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

2023: APC, PDP Na Fuskantar Babban Barazana A Yayin Da Peter Obi Ya Fara Kamfen A Arewa, Ya Ziyarci Dattijon Arewa Mai Karfin Fada A Ji

Shugaba Buhari.
Buhari Ga Yan Najeriya: Idan Da Kun San Wahalar Da Ake Sha A Wasu Kasashe Da Kun Godewa Allah. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar ya ce zai cigaba da yin iya kokarinsa don walwalar yan Najeriya bayan sauraron koke daga sarki da Gwamna Bello Aminu Masari na Katsina.

"Idan da mutanen mu sun san irin wahalar da ake sha a wasu kasashen Afirka a halin yanzu, da sun gode wa Allah bisa yanayin da ake ciki a nan gida.
"Muna kira ga mutane su kara hakuri, muna iya kokarin mu. Babu abin da ya fi zaman lafiya muhimmanci, wadanda ke kokarin kawo cikas ga zaman lafiyarmu, ko menene nufinsu, muna rokon Allah ya bamu basirar da za su yi maganinsu," in ji shi.

Game da nasarar Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na APC, Buhari ya jadada matakinsa na rashin zaben wanda zai gaje shi, yana mai cewa lokacin da batun ya taso, kimanin masu son takara 30 sun fito, mafi yawancinsu ministocinsa ne da gwamnonin jiha.

Kara karanta wannan

Fashin magarƙama: An kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje ɗauke da kayan laifi a Katsina

Buhari ya ce babu yadda za ta yi wu ya fifita wani cikinsu don haka ya umurci su tafi su yi abin da suke ganin ya fi dacewa kuma daga bisani suka zabi Bola Tinubu shi kuma ya zabi mataimakinsa.

Shettima: Yan Najeriya Sun Mayar Da Hankali Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Na Bunkasa Ta Fasaha

A wani rahoron, Sanata Kashim Shettima, abokin takarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023 ya ce su dena takaita tunaninsu kan addini yayin zaben shugabanni, rahoton The Cable.

Zaben Shettima da a matsayin mataimakin Tinubu ya janyo suka daga mutane saboda su biyu musulmi ne.

Da ya ke magana a ranar Juma'a yayin da ya karbi bakuncin tawagar APC karkashin jagorancin Mohammed Hassan, tsohon jakadan Najeriya a Amurka, tsohon gwamnan na Borno ya ce abin da ke gabansa da Tinubu shine sauya kasar.

Kara karanta wannan

Shettima: Yan Najeriya Sun Tattare Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Ke Kara Azama a Bangaren Fasaha

Asali: Legit.ng

Online view pixel