Wasu Maza Sanye Da Babban Riga Sun Tafi 'Yawon Sallah' Gidan Wani Attajiri Sun Sace Shi a Kogi

Wasu Maza Sanye Da Babban Riga Sun Tafi 'Yawon Sallah' Gidan Wani Attajiri Sun Sace Shi a Kogi

  • Wasu maza sun tafi gidan Alhaji Muhammed Jamiu Idris, mai gidan man Always Petroluem Energy Services sunyi awon gaba da shi
  • Kakakin yan sandan Jihar Kogi ya tabbatar da lamarin yana mai cewa mutanen sun tafi gidan Idris ne da sunan yawon sallah amma suka sace shi
  • Majiya daga iyalan Idris ta ce mazajen sun shiga gidan ne sannan suka fito da bindigu suka ce ya bi su kuma suka rika harbe-harbe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kogi - An yi garkuwa da Alhaji Muhammad Jamiu Idris, ciyaman/babban jami'i na gidan mai suna Always Petroleum Energy Services.

Daily Trust ta rahoto cewa an sace shi ne a gidansa da ke karamar hukumar Okene ta Jihar Kogi yayinda wasu maza da suka yi basaja a matsayin masu yawon sallah suka ziyarce shi.

Kara karanta wannan

An Tiso Keyar Maniyattan Kano 7 Daga Saudiyya Zuwa Najeriya Saboda Biza Ta Bogi

Muhammadu Idris.
Wasu Maza Sanye Da Babban Riga Sun Tafi 'Yawon Sallah' Gidan Wani Mai Gidan Man Fetur Sun Sace Shi a Kogi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiya daga iyalansa ta tabbatar da lamarin

Wani majiya daga iyalansa ta ce jim kadan bayan shiga gidan Idris, mazan sun fito da bindigu suka umurci ya bi su.

Majiyar ta ce masu garkuwar, wanda ke da manyan bindigu, sun rika harbe-harbe don firgita mutane wanda suka yi kokarin hana a tafi da shi.

An ce sun masa duka kafin su tafi da Idris, wanda shine shugaban Kungiyar Table Tennis na Arewa Ta Tsakiya.

Martanin yan sanda kan lamarin

Rundunar yan sandan Jihar Kogi ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa wadanda suka sace shin sun tafi gidansa ne jim kadan bayan sallar idi.

Kakakin yan sandan Kogi, SP William Ovye Aya, ya shaida wa Daily Trust cewa mutanen "su shida sanye da babban riga sun zo gaisuwan sallah ne wurin idris, da sunan su abokansa ne. Yayin ziyarar, suka sace shi zuwa wani wuri da ba a sani ba."

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Kakakin ya kara da cewa kwamishinan yan sanda Edward Egbuka ya umurci jami'ansa su bi sahun masu garkuwan su ceto Idris.

Kawo yanzu masu garkuwar ba su tuntubi iyalansa ba.

Gidan man Always Petroluem fitacce ne a Lokoja da kewaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164