Takardun kudi 8 mafi daraja a Afrika (Hotuna)
Ba kyan kudi bane amfaninsa a duniya. Yadda yake da daraja a kasar da kuma kasashen ketare shine darajar kudi. Ana kuwa gane darajar kudi ne ta wasu fuskokin a kasuwanci.
Dalar Amurka ce ake gani a matsayin kudin da ke da matukar daraja a duniya. A don haka ne ake amfani da ita wajen gwada darajar sauran kudade a duniya. Ga kudaden wasu kasashe a Afirka masu matukar daraja a 2019.
1.Dinar na kasar Libya
Dinar na kasar Libya ne kudi mafi daraja a nahiyar. Ana gwada darajarsa ne da yadda ake iya musaya da dalar Amurka da kuma abinda za ta iya siye. Dalar Amurka daya dai-dai take da dinarin Libya 1.38.
2. Dinar din kasar Tunisia
Dinarin kasar Tunisia ne kudin mai daraja ta biyu a Afirka. Dalar Amurka daya dai-dai take da dinarin kasar Tunisia 3.05
3. Cedis din kasar Ghana
Ghana ce kasar Afirka ta yamma daya tilo da ta samu shiga cikin jerin nan. Cedi din kasar Ghana 5.50 ne yake dai-dai da dalar Amurka 1.
4. Dinarin kasar Morocco
Dinarin kasar Morocco ne yazo na hudu a wannan jerin. Dinarin Morocco 9.55 ne yake dai-dai da dalar Amurka 1.
5. Pula na kasar Botswana
Kudin kasar Botswana ana kiransa da Pula. An kirkiro shi ne inda ya maye gurbin Rand na kasar Afirka ta kudu. Pula 10.60 ne yake dai-dai da dalar Amurka daya.
6. Kwacha na kasar Zambia
Kwacha ne kudin kasar Zambia. An kirkirosa ne inda ya maye pam na kasar Zambia. Kwacha 11.98 ne yake dai-dai da dalar Amurka daya.
7. Lilangeni na kasar Swazi
Lilangeni na kasar Swazi ne na bakwai a wannan jerin. Karfin musayar shi ne Lilangeni 13.99 dai-dai da dalar Amurka daya.
8. Rand na kasar Afirka na kudu
Rand na kasar Afirka ta kudu ne ya maye gurbin pam na kasar Afirka ta kudu. Rand 14.18 ne dai-dai da dalar Amurka daya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng