Yan bindiga sun kashe ‘ya’yan wani malamin addini a Adamawa, sun kuma yi awon gaba da diyarsa

Yan bindiga sun kashe ‘ya’yan wani malamin addini a Adamawa, sun kuma yi awon gaba da diyarsa

  • Tsagerun yan bindiga sun farmaki gidan Reverend Daniel Umaru na Cocin EYN da ke Njairi a karamar hukumar Mubi ta jihar Adamawa
  • Reverend Umaru ya rasa yaransa maza su biyu a harin yayin da yan bindigar suka yi awon gaba da diyarsa mace
  • Gwamna Ahmadu Fintiri ya yi Allah wadai da wannan hari sannan ya sha alwashin ganin an kamo masu laifin tare da hukunta su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Adamawa - Tsagerun yan bindiga sun kashe ‘ya’yan wani fasto biyu a jihar Adamawa sannan suka yi garkuwa da matashiyar diyarsa.

Gwamnatin jihar, wacce ta sanar da ci gaban a daren ranar Laraba, 6 ga watan Yuli, ta nuna damuwa kan lamarin, jaridar The Nation ta rahoto.

Fasto da iyalansa
Yan bindiga sun kashe ‘ya’yan wani malamin addini 2 a Adamawa, sun kuma yi awon gaba da diyarsa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yan bindigar sun farmaki gidan Reverend Daniel Umaru na cocin EYN a Njairi da ke karamar hukumar Mubi inda suka harbe shi sannan suka kashe yaransa biyu da kuma sace diyarsa mai shekaru 13.

Kara karanta wannan

Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

Gwamna Ahmadu Fintiri a wata sanarwa daga sakataren labaransa, Humwashi Wonosikou, ya yi Allah wadai da harin yan bindigar inda ya bayyana hakan a matsayin abun takaici.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ta ce:

“Gwamna Fintiri yayin da yake mika ta’aziyyarsa ga iyalin kan mutuwar 'ya'yan nasu, ya bayyana aikin yan bindigar a matsayin abin tsoro da dabbanci.
“Ya zama dole a hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki kuma dole mu bayar da cikakken gudunmawarmu ga hukumomin tsaro don aikata haka.”

Sanarwar ta ce gwamnati za ta ci gaba da magance laifuka ta kowani bangare ciki harda barazanar da yan bindigar ke yi, rahoton Daily Trust.

Fintiri ya kuma umurci hukumomin tsaro da su tattara bayanan sirri sannan su gano masu laifin don fuskantar shari’a.

Harin gidan yarin Kuje: An girke tsauraran matakan tsaro a garuruwan Kuje da kewaye

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji da 'yan sa kai sun bindige 'yan ta'adda 8 a wata musayar wuta

A wani labari na daban, mun ji cewa an tsaurara matakan tsaro a yawancin yankuna da ke garuruwan Kuje a babbar birnin tarayya Abuja, bayan farmakin da yan bindiga suka kai cibiyar gyara hali na Kuje a daren ranar Talata, 5 ga watan Yuli.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa wakilinta ya kewaye yankin inda ya tarar da jami’an tsaro dauke da manyan makamai a wurare masu muhimmanci.

NAN ta rahoto cewa an girke motocin yaki a kewayen mahadar gidan yarin na Kuje, yayin da tawagar jami’an tsaro ke ta shawagi a motocin fatrol.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng