Ba sai kun biya ba: Matukin adaidaita sahu dake daukan masu juna biyu kyauta ya birge jama'a

Ba sai kun biya ba: Matukin adaidaita sahu dake daukan masu juna biyu kyauta ya birge jama'a

  • Wani matukin keke napep wacce aka fi sani da adaidaita sahu mai taushin zuciya ya sha addu'o'i daga 'yan Najeriya bayan kyan halinsa ya bayyana
  • Lamarin ya fara ne bayan da wani mutum ya hau keke napep din kuma ya ga rubutun da ya manna a gaban adaidaita sahunsa
  • A rubutun, an umarci duk wata mace dake dauke da juna biyu da ta hau adaidaita sahun ba tare da ta biya ko sisin ta ba saboda tausaya musu da yake yi

Wani matukin keke napep ya matukar taba zukatan mutane da kyan halinsa da ya bayyana inda 'yan Najeriya a kafar sada zumuntar zamani suka dinga kwarara masa yabo da addu'o'i.

Wani 'dan Najeriya mai suna Afrosix AJ Jaara ya wallafa abinda ya gani rubuce a cikin keken da ya shiga a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bikin 'yancin kai ya zo da tsaiko a Amurka, 'yan bindiga sun harbe jama'a

Matukin adaidaita sahu dake daukar masu juna biyu kyauta
Ba sai kun biya ba: Matukin adaidaita sahu dake daukan masu juna biyu kyauta ya birge jama'a. Hoto daga Afrosix AJ Jaara, Daily Post
Asali: Facebook

Rubutun da aka manna a saman keke napep din ta ce, "Wannan keke kyauta ne ga duk mata masu juna biyu."

Afrozix wanda yace yana hanyarsa ta zuwa coci ne yayin da ya hau napep din yayi addu'a Ubangiji ya sanya albarkarsa ga matukin keke napep din.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kwatanta rubutun da kayataccen rubutu kuma abun so.

'Yan Najeriya sun yi martani

Babu dadewa da yin wannan wallafa, 'yan Najeriya suka garzaya sashin tsokaci inda suka dinga kwarara addu'o'i da yabo ga matukin keke napep din.

Victoria Kelechi tace: "Na hadu da wasu yayin da nake da juna biyu. Ubangiji ya sanya musu albarka."
Olukriz yace: "Ba wai dole sai kana da komai sannan zaka yanke hukuncin taimako ba. Wannan shi ne misali mai kyau."
Comr Moses Itaketo yace: "Wannan matukin keken yana da labarin bayarwa wanda nake tsammanin shiyasa yake hakan. Ubangiji zai dinga amsa addu'arsa a kodayaushe."

Kara karanta wannan

Jirgin kasan Abj-Kd: Shehu Sani da iyalan fasinjojin da aka sace zasu fito zanga-zanga

Ozoemena Jennifer tace: "Wannan abun da yayi yafi tsakaninsa da Ubangiji a kan abinda kuke gani. Yana da kyakyawan dalilin yin hakan. Ubangiji ya bashi duk abinda zuciyarsa take so, Ameen."
Nonye Maurice Onuoha-Nwachukwu cewa yayi: "Tabbas na taba haduwa da daya a Fatakwal. Baya karbar kudi daga masu juna biyu."

Yadda Soja ya Harbe Mai Siyar da Man Fetur Har Cikin Gidan Mai a Minna

A wani labari na daban, wani soja, wanda ba a ambaci sunansa ba ya halaka mai bada mai a gidan man Shafa a Minna, babban birnin jihar Neja.

Lamarin ya auku ne a rashen gidan man Shafa na titin Bosso, jaridar The Nation ta ruwaito.

An gano yadda lamarin ya auku yayin da mai bada man ya yi kokarin shiga rikicin da ya barke tsakanin manajansa da sojan.

Sai dai, an tattaro yadda sojan suka samu sabani da manajan gidan man, wanda ya rikide zuwa cacar bakin da ta kai ga biyun marin junansu.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya sake jan-kunnen magoya baya, ya nuna masu hanyar farauto zuciyar mutane

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel