Yadda Soja ya Harbe Mai Siyar da Man Fetur Har Cikin Gidan Mai a Minna

Yadda Soja ya Harbe Mai Siyar da Man Fetur Har Cikin Gidan Mai a Minna

  • Wani soja ya bindige mai siyar da man fetur a gidan man Shafa reshen Minna dake jihar Neja yayin da wani rikici ya barke tsakanin sojan da manajan gidan man
  • An tattaro yadda wanda lamarin ya auku dashi ya yi wa sojan barazana da adda tare da fushi da fushin ubangidansa, wanda rikici ya barke tsakaninsu har ta kai su ga musayar mari
  • Sai dai, nan take sojan ya fiddo da bindiga ya bindige matashin inda aka garzaya da shi asibiti wanda ko kafin isarsu rai ya yi halinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Minna, Niger - Wani soja, wanda ba a ambaci sunansa ba ya halaka mai bada mai a gidan man Shafa a Minna, babban birnin jihar Neja.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Mai Kwashe Shara Dake Karbar N50 Kudin Aikinsa Ya Gigice Bayan An Bashi Kyautar N50k

Lamarin ya auku ne a rashen gidan man Shafa na titin Bosso, jaridar The Nation ta ruwaito.

Taswiar jihar Niger
Yadda Soja ya Harbe Mai Siyar da Man Fetur Har Cikin Gidan Mai a Minna. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An gano yadda lamarin ya auku yayin da mai bada man ya yi kokarin shiga rikicin da ya barke tsakanin manajansa da sojan.

Sai dai, an tattaro yadda sojan suka samu sabani da manajan gidan man, wanda ya rikide zuwa cacar bakin da ta kai ga biyun marin junansu.

Ganau sun bayyana yadda mai bada man, wanda ya harzuka matuka bisa halayyar sojan, ya ciro adda gami da yi wa sojan barazana.

Yayin da yake barazana da addar ga sojan ba tare da taba shi ba, sojan ya fiddo da bindigarsa gami da bindige mai bada man fetur din.

The Nation ta fahimci yadda aka garzaya da yaron babban asibitin Minna, sai dai ko kafin a isa rai ya yi halinsa.

Kara karanta wannan

Yadda Ango Ya Sheka Barzahu a Kokarin Hana 'Yan Bindiga Sace Matarsa Mai Ciki

Ma'aikata asibitin sun ce an tabbatar da rasuwar mai bada man fetur din yayin da aka kai shi asibitin.

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da siffanta hakan a matsayin mummunan lamari.

A cewarsa, ana cigaba da bincikar mummunan lamarin, sannan an tura tawagar bincike yankin tare da ganin an kwantar da tarzomar.

An rufe gidan man a halin yanzu.

Sai dai Abdullahi Shehu, mazaunin yankin kuma wanda lamarin ya faru a gaban shi ya sanar da Legit.ng cewa, mai siyar da man ya sokawa soja daya wuka a hannu kuma ya dauko adda yana masa barazana da ita.

Wani soja na daban ne ya dauko bindiga ya harbe shi ganin jini yana zuba daga hannun sojan da aka sokawa wuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel