Jirgin kasan Abj-Kd: Shehu Sani da iyalan fasinjojin da aka sace zasu fito zanga-zanga

Jirgin kasan Abj-Kd: Shehu Sani da iyalan fasinjojin da aka sace zasu fito zanga-zanga

  • Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa, zai fito tare da iyalan fasinjojin jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna domin zanga-zanga
  • Ya koka da halin da fasinjojin suke ciki inda yace akwai takaici ganin iyayenmu, 'yan uwanmu mata da maza a hannun 'yan ta'adda
  • Ya sanar da cewa zai ara muryarsa ta yadda za a yi kira ga gwamnatin tarayya domin ta gaggauta ceto rayukan wadanda aka sacen

Kaduna - A ranar Talata mai zuwa, wadanda lamarin ya ritsa dasu zasu cika kwanaki 100 a hannun masu garkuwa da mutane.

Shehu Sani, wanda shine shugaban Civil Rights Congress, ya sha alwashin bayyana a yayin zanga-zangar domin ara muryarsa wurin kira ga gwamnati da ta dauka mataki yanzu ba sai daga baya ba saboda rayukan wadanda aka sace, wadanda yace suna fama da wahalar da bata misaltuwa a cikin daji.

Kara karanta wannan

Hukuncin namijin da yaci amanar matarsa bisa kundin tsarin mulkin Najeriya

The Nation ta ruwaito cewa, a yayin jawabi lokacin taro da iyalan wadanda aka sacen a Kaduna, Sanata Sani yace, "matukar suna hannun 'yan ta'adda, jama'ar arewa maso yamma da dukkan kasar ba zasu taba zama cikin kwanciyar hankali ba.
"Ku kwatanta yadda mace mai shekaru 85 ke rayuwa dasu a daji, a wannan lokacin damina, dole rayuwa da dabbobi da macizai. Kwanciyar hankalinmu da zaman lafiyanmu ya ta'allaka ne ga samun 'yancinsu.
"Abun takaici ne yadda kasa mai mutane sama da miliyan 211 da kuma ke zuba kudi a bangaren tsaro amma ta kasa ceto wadannan mutanen.
"Rayuwarsu rayuwar mu ce, halin da suke ciki na bayyana halin da kasar ke ciki. Idan ba zasu iya bacci ba, mu ma ba za mu iya ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yanzu cikin watanni ukun nan muna cikin tashin hankali, duk saboda halin da iyayenmu mata, kannanmu mata da maza da 'ya'yanmu ke ciki."

Kara karanta wannan

Bauchi: Yadda dattijuwa mai shekaru 52 ta rasa ranta yayin kare 'danta daga 'yan bindiga

Ya kara da jinjinawa wadanda ke kokarin sasanci tsakanin gwamnati da 'yan bindigar kuma yayi kira gare su da kada su ja baya har sai an sako dukkan wadanda aka sace.

A yayin bada labarin halin da wadanda aka sace suke ciki ga Sanata Sani, shugaban iyalan wadanda aka sace, Dr. Abdulfatah Jimoh yace, tun bayan da aka sako wasu daga cikin wadanda aka sace a makonni uku da suka gabata, bayanan da suka tattaro sun nuna cewa sauran suna cikin mawuyacin hali.

Kamar yadda yace, suna kwanciya a tsakar rana, kasan ruwan sama kuma muhalli mai cike da hatsari.

"Mun yi duk abinda zamu iya domin ceto su amma a yanzu mun yanke hukuncin fitowa zanga-zangar domin tirsasa gwamnatin tarayya ta dauka matakin gaggawa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel