2nd Class: Yadda dan fursuna ya gwama zaman kaso da karatun jami'a, kuma ya ba da mamaki

2nd Class: Yadda dan fursuna ya gwama zaman kaso da karatun jami'a, kuma ya ba da mamaki

  • Wani fursuna ya ba da mamaki yayin da ya kammala karatunsa na digiri lokacin da yake daura a magarkamar Abuja
  • Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, ya kammala karatunsa da sakamako mai kyau, lamarin da ya ba da mamaki
  • Yayin da ake ba shi takardar kammala digiri, ya bayyana manufarsa ta gaba da kuma yadda ya shirya

Kuje, Abuja - Wani fursuna a gidan gyaran hali na Najeriya da ke Kuje, Mista Chinwendu Heart, ya kammala karatun digiri da sakamako mai kyau (2nd Class) a fannin ilimin Theology daga jami'ar NOUN da ke kan yanar gizo.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Mista Chukwuedo Humphrey ya fitar ranar Laraba a Abuja 29 ga watan Yuni, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bata-gari: An kama 'yan mata 20 da samari 14 da ke rawar badala a jihar Gombe

Karatu ya samu daga wani fursuna da ke zaman gidan yari
2nd Class: Yadda dan fursuna ya hada zaman kaso da karatun jami'a, ya gama da sakamako mai kyau | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Humphrey ya ruwaito, NOUN, Dokta Angela Okpala, wacce ta ba da takardar shaidar kammalawar a ranar Talata, inda ta karfafa wa daliban da suka kammala karatun kwarin gwiwar zama jakadun jami’ar nagari da kuma masu kwaazo.

Da yake magana, Mista Ibrahim Shehu, jami’in da ke kula da gidan yari ta Kuje, ya ce fursunan ya nuna hali na kwarai a tsawon lokacin karatunsa, Pulse ta kawo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Fursuna ya kasance mai himma a karatunsa kuma ya yi rayuwa mai kyau a tsare."

Shehu ya umarci sauran fursunonin da su yi amfani da damar samun ilimi kyauta daga NOUN su inganta kansu, ya kara da cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban dan Adam.

Shi kuwa wanda ya kammala karatunsa, Heart ya nuna farin cikinsa, inda ya ce ya shigo Cibiyar Gyaran Hali ta Kuje ne ba tare da takardar shaidar kammala sakandare ba.

Kara karanta wannan

Kogi: Tanka Dauke da Man Fetur Tayi Bindiga, Ta Halaka Rayuka 3 a Lokoja

Heart ya ce da kwarin gwiwar ma’aikatan yanzu ya samu digiri kuma yana fatan ya yi amfani da damar da NOUN ta bashi don samun digiri har na na uku.

Ya kuma kara karfafa wa sauran fursunonin da su tsunduma kansu cikin wadannan tsare-tsare na kawo sauyi a gidan yari a maimakon zama dirsham a cikin gidan gyaran hali.

Kotu ta yi watsi da batun ba da belin shugaban IPOB Nnamdi Kanu

A wani labarin, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar neman belin shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, Channels Tv ta ruwaito.

Mai shari’a Binta Nyako, a hukuncin da ta yanke a ranar Talata, ta ce batun cin zarafi ne ga tsarin kotun da kuma yunkurin kawo cikas ga ci gaba da shari’a kan batutuwan da ke gaban kotun.

Sai dai ta shawarci wanda ya shigar da kara ya tunkari kotun daukaka kara kan batun belin, idan bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kama wanda ya harbe tsohon hadimin Jonathan, Ahmad Gulak

Asali: Legit.ng

Online view pixel