Da dumi-dumi: Kotu ta yi watsi da batun ba da belin shugaban IPOB Nnamdi Kanu

Da dumi-dumi: Kotu ta yi watsi da batun ba da belin shugaban IPOB Nnamdi Kanu

  • Babban kotun tarayya a Abuja ta ki amincewa da batun sakin Nnamdi Kanu bisa beli saboda wasu dalilai
  • A baya Nnamdi Kanu ya sha bayyana bukatar beli a gaban kotu, amma mai shari'a da gwamnati suka yi ta turjiya
  • Hujjojin da ake gabatarwa a gaban kotu sun hada da tserewar da Nnamdi Kanu ya yi lokacin da ya samu beli a 2017

FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar neman belin shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, Channels Tv ta ruwaito.

Mai shari’a Binta Nyako, a hukuncin da ta yanke a ranar Talata, ta ce batun cin zarafi ne ga tsarin kotun da kuma yunkurin kawo cikas ga ci gaba da shari’a kan batutuwan da ke gaban kotun.

Kara karanta wannan

Kada wanda ya fito yau, IPOB ta umarci yan jihohin Igbo

Sai dai ta shawarci wanda ya shigar da kara ya tunkari kotun daukaka kara kan batun belin, idan bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba.

An hana belin Nnamdi Kanu
Da dumi-dumi: Kotu ta yi watsi da batun ba da belin shugaban IPOB Nnamdi Kanu | Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Alkalin kotun ya bayyana cewa tun daga lokacin da aka yanke hukunci a Yulin 2017 ta belin Kanu ya zuwa yau, an dage karar har sau 15 kuma har yanzu ba a ci gaba da sauraren karar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kara da cewa ba ta gamsu da dalilin da shugaban kungiyar ta IPOB ya bayar na rashin gurfana a gaban kotu domin ci gaba da shari'ar sa ba, Punch ta ruwaito.

Mai shari’a Nyako ta bayyana cewa daga bayanan kotun, Kanu ya samu wakilcin lauyansa a ranar da aka soke belinsa, haka kuma wadanda za su tsaya masa, kuma ba a taba kin sauraransa ba ko yi masa adalci.

Ta dage cewa dole ne shugaban na IPOB ya bayyana dalilin da ya sa ya karya ka'idar belin da aka ba shi a baya kafin ya samu wata kwakkwarar hujjar samun wani belin.

Kara karanta wannan

Malaman addini: Ku dai bi hukuncin da kotu ta yanke kan dokar sanya hijabi

Bayan haka, an dage sauraren karar har zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba domin jiran sakamakon karar da Kanu ya shigar a kotun daukaka kara.

Hukuncin na ranar Talata ya zo ne wata guda bayan da kotun ta ki sakin shugaban kungiyar ta IPOB kan beli a ranar 18 ga watan Mayu.

Nnamdi Kanu ya kusa makancewa, Lauyansa ya bayyanawa kotu

A wani labarin, sabon lauyan da ke tsayawa shugaban kungiyar yan tawayen IPOB Nnamdi Kanu a kotu, Chief Mike Ozekhome(SAN), ya bayyana cewa ciwon idon Kanu ya tsananta.

Mike Ozekhome, ya bayyana hakan yayin zaman kotu na ranar Laraba, 16 ga Febrairu, 2022, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, idan ba'a dau matakin gaggawa ba, Nnamdi Kanu zai makance a hannun hukumar DSS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel