Yan Bindiga Sun Kashe Yan Bijilante Da Mafarauta 5 Da Suka Tafi Daji Don Ceto Manoma 22 Da Aka Sace a Niger

Yan Bindiga Sun Kashe Yan Bijilante Da Mafarauta 5 Da Suka Tafi Daji Don Ceto Manoma 22 Da Aka Sace a Niger

  • Yan bindigan sun halaka yan bijilante guda biyar da mafarauci daya a hanyarsu na zuwa daji domin ceto mutane 22 da aka sace daga gonakinsu
  • Daya daga cikin yan bijilanten da ke cikin tawagar da aka kai wa harin, ya sha da kyar, ya ce suna dafa da shiga dajin kawai suka ji ruwan harsashi
  • Ya kara da cewa yan bindigan sun boye a wurare daban-daban har da kan bishiya ne suka jira zuwansu kuma suka bude musu wuta, ya tabbatar mutum 6 sun mutu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Niger - Yan bindiga sun harbe yan bijilante biyar har lahira da wani mafarauci daya a wani harin kwantar bauna da suka kai musu a dajin Lafiya-Kpada-Duma a Jihar Niger.

Daily Trust ta gano cewa wasu yan bijilante shida sun tsira da raunin bindiga sakamakon harin.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun ceto wasu mutane 14 da aka yi garkuwa da su a dajin Zamfara

Yan Bindiga.
Yan Ta'adda Sun Kashe Yan Bijilante Da Mafarauta 5 Da Suka Tafi Daji Don Ceto Manoma 22 Da Aka Sace a Niger. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani dan bijilante wanda ke cikin tawagar wanda ya nemi a boye sunansa ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma'a bayan an gayyato yan bijilante daga Abuja da Niger don ceto wasu manoma 22 da aka sace a gona a kauyen Rafin-Daji a karamar hukumar Abaji na FCT, a ranar Laraba.

Ya ce yan bijilanten da mafarautan sun daf da shiga dajin ne daga garin Laifya Kpdada-Duma, sai yan ta'addan suka bude musu wuta.

A cewarsa, wasu daga cikin yan bindigan sun boye ne a kan bishiya kuma da ganin yan bijilanten suka bude musu wuta suka kashe biyar cikinsu har da mafarauci.

"Ruwan harsashi suka mana lokacin da suka mana harin kwantar bauna, wasunsu na zaune kan bishiya. Da ganinmu, suka bude wuta. Ba zan iya cewa ga yadda na tsira ba," in ji shi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama

Majiyar ta kara da cewa yan bijilante biyar da mafarauci daya sun mutu saboda sun rasa jini, yana mai cewa hanyar dajin Yaba bai da kyau don haka ba a iya kai su asibiti ba kan lokaci.

Wakilin Daily Trust wanda ya ziyarci Babban Asibitin Abaji ya ce ga yan bijilante shida da raunin bindiga, likitoci na musu magani yayin da abokai da yan uwa ke tururuwan zuwa gaishe su.

Kakakin yan sandan FCT, Abuja, ASP Oduniyi Omotayo bai riga ya ce komai kan lamarin ba domin bai amsa sakon text da aka masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daya daga 'yan matan Chibok: Na san marigayi Shekau, sauran mata 20 a hannun BH

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.

Sace basaraken na zuwa ne kwanaki uku bayan sace wani kwararren masanin kimiyyan magunguna, AbdulAzeez Obajimoh, shugaban kamfanin magunguna na AZECO Pharmaceutical da ke Ozuwaya a Okene, yankin Kogi Central.

Asali: Legit.ng

Online view pixel