Bayan Halasta Saka Hijabi, Lauya Mai Addinin Gargajiya Ya Tafi Kotun Koli Sanye Da Tufafin Bokaye

Bayan Halasta Saka Hijabi, Lauya Mai Addinin Gargajiya Ya Tafi Kotun Koli Sanye Da Tufafin Bokaye

  • Barista Malcolm Omoirhobo, wani lauya mai kare hakkin bil adama a ranar Alhamis ya tafi kotun koli da tufafi mai kama da na bokaye
  • Omoirhobo, wanda ya ce shi mai addinin gargajiya ne ya ce ya saka tufafin ne domin hukuncin da kotun koli ta yanke kan hijabi a Legas inda ta hallasta saka tufafi na addini a makaranta da kotu
  • Lauyan, bayan godiya ga kotun kolin ya ce daga yanzu irin tufafin da zai rika saka wa kenan domin shi mabiyin 'Olokun' ne Ubangijin Rafi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Lauya mai kare hakkin bil adama, Malcolm Omoirhobo, a ranar Alhamis, a ranar Alhamis ya kwashi yan kallo saboda irin tufafin da ya saka yayin zuwa kotun koli a Abuja, rahoton The Punch.

Hotunan da aka yada a dandalin sada zumunta sun nuna Omoirhobo sanya da tufafin lauya hade da wasu abubuwa da suka yi kama da na masu maganin gargajiya ko bokaye.

Kara karanta wannan

Za a shirya wasan kwaikwayo a kan tarihin tsige Sanusi I da Sanusi II a 1963 da 2020

Malcolm Omoirhobo
Hukunci Kan Hijabi: Dirama A Yayin Da Lauya Ya Saka Tufafin Irin Na Boka Zuwa Kotun Koli. Hoto: @Florence_Esq.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lauyan ya saka sarka ta 'cowries' a wuyansa da fuka-fiki a kansa da wasu abubuwa a kafansa.

A cewarsa, ya saka tufafin ne don nuna godiya ga Kotun Koli wacce a ranar Juma'a 17 ga watan Yuni ta halastawa dalibai mata na makarantun sakandare na gwamnati saka hijabi a Legas.

A jawabin da ya yi wa manema labarai:

"Na yi matukar godiya da hukuncin kotun kolin. A ranar Juma'a da ta gabata, sun yanke hukunci mai muhimmanci da ya goyi bayan sashi na 38 na kundin tsarin mulki. Shine damar mu na tunani da riko a abu a zuciyan mu da addini.
"Cewa muna da ikon bayyana addinin mu a makarantu da kotu. Wannan hukuncin da suka yi a ranar Juma'a ne ya karfafa min gwiwa.
"Saboda ni addinin gargajiya na ke yi kuma haka na ke ibada. Bisa hukuncin kotun kolin, haka zan rika saka tufafi a kotu domin ni mabiyin 'Olokun' ne Ubangijin Rafi."

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Akwai wasu miyagun mutane da ke shirin sanya Najeriya cikin garari

Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN

A wani rahoton, kungiyar Kirista ta Nigeria, CAN, ta bukaci gwamnatin tarayya da Sufeta Janar na Yan sanda su saka baki kan rikicin Hijabi da ake yi a wasu makarantu da ke jihar Kwara, rahoton Daily Trust.

A sanarwar da ta fitar a ranar Laraba, Sakataren CAN na kasa, Joseph Bade Daramola ya ce kungiyar ta gano cewa gwamnatin jihar Kwara ta bada umurnin bude makarantun da aka rufe ta tare da warware rikicin ba.

Ya ce hakan yasa wasu da ake zargin yan daba ne sun kai hari wasu coci-coci da makarantun mission sunyi barna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel