Al’ummar jihar Neja sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya da yan bindiga

Al’ummar jihar Neja sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya da yan bindiga

  • Wasu yankunan Kusherki dake karamar hukumar Rafi ta jihar Niger sun fara yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan bindiga da suka addabesu
  • Kamar yadda shugaban yankin Kusherki ya sanar, sun aike da wakilansu domin tattaunawa da 'yan bindigan
  • Sun kuma yanke musu N2m na goro wanda zasu rabawa kungiyoyin 'yan bindigan shedar zaman lafiya
  • Shugaban karamar hukumar Rafi, yace ba za su hana jama'a yarjejeniyar zaman lafiyan ba illa iyaka su taimaka musu wurin hada kudaden da 'yan bindigan ke bukata

Rafi, Niger - Mazauna yankunan da ta'addancin 'yan bindiga yayi kamari a yankin Kusherki na karamar hukumar Rafi ta jihar Niger sun nemi zaman lafiya da 'yan bindiga.

Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan bindigan suka bukaci a yi yarjejeniyar zaman lafiya da mazauna yankin tare da sharadin cewa ba zasu dinga kai su kara wurin hukuma ba duk lokacin da suka ketare yankunansu.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Sake Jaddada Cewa Sai An Ladabtar Da 'Yan Ta'adda, Ya kwatantasu da Ragwaye

Shugaban yankin Kusherki, Alhaji Garba Kusherki, ya sanar da Daily Trust cewa tuni suka tura wakilai domin tattaunawa da 'yan bindigan.

Yan bindiga
Al’ummar jihar Neja sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya da yan bindiga Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya kara da bayyana cewa, 'yan bindigan sun bukaci N2m domin siyan goro wanda zasu raba a tsakanin abokai da 'yan uwa domin su san cewa an yi yarjejeniyar zaman lafiya da mutanen yankin, tare da alkawarin dawowar zaman lafiya idan aka kiyaye sharuddansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kusherki ya ce:

"Idan Allah ya nuna, a ranar Alhamis 'yan bindigan sun kira mu inda suka bayyana mana cewa suna son a yi yarjejeniyar zaman lafiya. Don haka muka aika wakilai da zasu hadu da su kusa da dajin Birnin Gwari a jihar Kaduna. Sun bukaci wakilanmu da su tsaya a Maganda sannan su je su dauke su.
"A karshe, sun sanar da mu cewa mune silar fadansu da kuma yankunanmu. Sun ce duk lokacin da jama'a suka gansu suna wucewa da shanu, sai su yi musu kwanton bauna tare da fara kai musu hari. Duk da kuwa shanun satan ba na jama'ar yankin bane don haka ba su ga dalilin da zai sa su hare su ba. A don haka ne suka yanke hukuncin daukar fansa."

Kara karanta wannan

An kashe akalla mutum 16 a sabon harin da aka kai jihar Benue

Ya kara da cewa:

"Da yawa daga cikin wadanda suke kashewa maza ne. Sun kashe sama da maza 30. Bayan kashe maza, suna garkuwa da matanmu da kananan yara.
"Sun ce bayan yarjejeniyar nan ta zaman lafiya, babu wata kungiyar 'yan bindiga da za ta sake kai hari yankinmu kuma idan wata kungiyar tayi, zasu gano ta tare da daukar mataki. Amma dole ne mu iya tattaro kudi koda kuwa bai kai yadda ake bukata ba. Muna bukatar taimakon su."

Kusherki ya kara da cewa, babban limamin Unguwan-Barmo da wasu mutum 20 da suka hada da mata 10 sun shaki iskar 'yanci a ranar Talata a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiyan.

Yace:

"Sun ce idan kudi suke so, zasu cigaba da karbar kudin fansa. Sun ja kunnenmu kan mu daina kai musu hari duk lokacin da muka gansu amma idan muna son fada da su, sun shirya cigaba da fada har nan da shekara 10."

Kara karanta wannan

Ganau: 'Yan bindiga sun bindige 'yan sanda 6 a yunkurin sace mahajjata a Sokoto

Shugaban yankin ya koka kan rashin tsaro da taimakon al'umma daga jihohi da gwamnatin tarayya, inda yace shugaban karamar hukumar Rafi, Alhaji Isma'ila Modibo ne yake taimaka musu.

Shugaban ma'aikatan shugaban karamar hukumar, Mohammed Mohammed, yace karamar hukumar ta san da yarjejeniyar zaman lafiya da ake yi tsakanin 'yan bindigan da mazauna yankunan.

Yace yankunan Kusherki suna fama da hare-hare saboda suna da iyaka da Birnin Gwari ta jihar Kaduna wacce ta kasance hanyar wucewar 'yan ta'addan na tsawon shekaru.

Ya kara da cewa:

"Amma shugaban karamar hukuma ya shawarce mu da cewa kada mu hana wannan yarjejeniyar ta zaman lafiya saboda zasu cigaba da kai farmaki ta yadda karamar hukumar ba za ta iya yi musu wani abu ba. A lokacin da bukatar mu taimaka musu da abinda zasu bai wa 'yan bindigan, sai mu taimaka."

‘Yan sanda sun ceto wasu mutane 14 da aka yi garkuwa da su a dajin Zamfara

Kara karanta wannan

Hajjin Bana: Maniyyatan da aka yi Garkuwa dasu a Sokoto Sun Samu 'Yanci

A wani labari, rundunar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa jami’anta sun ceto wasu mutane 14 a yayin wani aiki da suka gudanar a dajin Kunchin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa an yi garkuwa da mutanen ne daga garuruwansu da ke Nasarawa Wanke da Rijiya a karamar hukumar Gusau.

Sun shafe tsawon kwanaki 42 a tsare kafin aka ceto su a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng