‘Ka je Atiku ya baka kudin’: Matashi ya kwace kudin da ya baiwa mahaifinsa saboda ya ki goyon bayan Peter Obi

‘Ka je Atiku ya baka kudin’: Matashi ya kwace kudin da ya baiwa mahaifinsa saboda ya ki goyon bayan Peter Obi

  • Babban zaben Najeriya da za a yi a 2023 ya hado wani matashi da mahaifinsa kan dan takarar shugaban kasa da kowannensu yake so
  • Matashin ya baiwa mahaifin kyautar kudi sannan sai ya tambaye shi game da dan takarar da yake goyon baya
  • Sai kuma ya karbe kudin da ya baiwa mahaifin nasa saboda ya ce ya fi son Atiku cikin yan takarar

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar bidiyon wani matashi da mahaifinsa a shafukan soshiyal midiya.

A cikin bidiyon dai wani matashi ne ya baiwa mahaifinsa kyautar kudi sai kuma ya karbe abin sa saboda uban nasa baya goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi.

Dan gajeren bidiyon wanda shafin @bcrworldwide ya wallafa a Instagram ya fara ne da nuna matashin yana mika wa mahaifin nasa damin kudi.

Kara karanta wannan

2023: Makomar 'Dan Takarar APC, Bola Tinubu a Jihohi 19 na Arewacin Najeriya

Atiku, Obi da wani dattijo
‘Ka je Atiku ya baka kudin’: Matashi ya kwace kudin da ya baiwa mahaifinsa saboda yak i goyon bayan Peter Obi Hoto: @bcrworldwide
Asali: Getty Images

Da mahaifin nasa ya tambaye shi dalilin basa kyautar kudin, sai matashin ya ce kawai yana so ya yi amfani da kudin ne wajen kula da kansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Laifin mahaifin shine zabar Atiku

Sai dan ya tambayi mahaifin nasa wa zai zaba a zaben shugaban kasa na 2023.

Mahaifin ya ambaci Atiku Abubakar, Peter Obi da Bola Tinubu amma sai ya zabi dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda a cewarsa shi ke da damar lashe babban zaben na shekara mai zuwa.

Sai matashin ya nemi mahaifin nasa ya mika masa kudin da ya bashi tun farko. Da ya damki kudinsa, sai ya umurci mahaifinsa ya je ya samu Atiku ya bashi kudin sannan ya bar wajen.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

@duch_peter ya ce:

“Kada ka bashi kowani kudi wahala bai ishe shi ba.”

Kara karanta wannan

Ka ji da matsalolin da ke kanka: Martanin Tinubu ga Atiku kan shaguben abokin takara

@@mhiz_maris_maris ya ce:

“Ji abun da wannan mutumin ke fadi tunubu ya fi dama...wa ke ambatan sunan wannan makashin na...Peter Obi ko ba kowa dan Allah.”

@wittyirene78 ya ce:

“Iyayenmu ne suka jefa mu cikin wannan halin sannan kuma suna so su sake zabar wadannan tsoffin. Wani irin wahala ne wannan?”

2023: Budurwa ta rabu da saurayinta saboda baya goyon bayan Peter Obi ya gaje Buhari

A wani labarin, mun ji cewa wata matashiyar budurwa mazauniyar birnin Abuja wacce aka ambata da suna Josephine ta rabu da saurayinta saboda ya ki goyon bayan dan takarar shugaban kasar da take so gabannin babban zaben 2023.

Josephine ta wallafa a shafinta na twitter cewa ita yar kashenin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi ne.

Da take bayyana masoyin nata a matsayin ‘wawa’, matashiyar ta ayyana cewa ba za ta iya ci gaba da soyayya da mutum kamar wannan ba musamman tunda ya ki bin sahun dan takarar shugaban kasa mafi soyuwa a wajenta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan jinya a Landan, an sallami tsohon shugaban Najeriya a asibiti

Asali: Legit.ng

Online view pixel