Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun fille kan wani tsohon dan majalisa

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun fille kan wani tsohon dan majalisa

  • Wasu ‘yan bindiga sun sare kan wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Anambra, Nelson Achukwu
  • An sace Achukwu a ranar 9 ga watan Yunin 2022 daga gidansa da ke Ukpor, karamar hukumar Nnewi ta kudu
  • Maharan sun kashe tsohon dan majalisar ne bayan yan uwansa sun biya naira miliyan 15 a matsayin kudin fansarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Anambra - Tsagerun yan bindiga sun fille kan Nelson Achukwu, wani tsohon dan majalisa a jihar Anambra, jaridar Independent ta rahoto.

An tattaro cewa yan bindiga sun sace Achukwu daga karamar hukumar Nnewi ta kudu da ke jihar Anambra yan watanni da suka gabata bayan sun zarge shi da kaiwa hukumomin sojoji kwarmato.

Sai dai kuma, an sake shi bayan wadanda suka yi garkuwa da shi sun gano cewa bai da laifi a zargin da suke masa.

Kara karanta wannan

An Gano Mabuyar Yan Ta'adda A Jihohin Niger Da Kwara, Majalisar Dattawar Najeriya

Tsagerun yan bindiga
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun fillewa wani tsohon dan majalisa kai Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An sake sace Mista Achukwu, wanda ke da nakasa, kimanin makonni uku da suka gabata daga gidansa da ke garin Mkpor.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tattaro cewa an fille masa kai bayan iyalinsa sun biya yan bindigar naira miliyan 15 a matsayin kudin fansarsa.

Kakakin yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da lamarin a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni, jaridar Premium Times ta rahoto.

Ya ce an gano gawar tsohon dan majalisar ne a ranar Talata a tsakanin iyakar Uke da Ukpor a yankin.

Mista Ikenga ya ce:

“An tsinci gawar tsohon dan majalisar ne a bayan kogin Ulasi kuma yan uwansa sun gaggauta binne shi a yammacin ranar Talata kasancewar gawar ta fara rubewa.
“Ana ta kokarin ganin an ceto shi daga hannun wadanda suka sace shi kafin wannan mummunan al’amari.”

Kara karanta wannan

Daya daga 'yan matan Chibok: Na san marigayi Shekau, sauran mata 20 a hannun BH

Kakakin yan sanda ya ce yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba a binciken lamarin da kuma tabbatar da ganin cewa an gano makasan.

Mista Achukwu ne mamallakin gidan mai na Nelly Oil & Gas da ke Utuh, wani gari a yankin.

Sabon hari: Mutum 10 sun mutu, 5 sun hallaka a harin 'yan ta'adda a jihar Benue

A wani labarin, mun ji cewa akalla gawarwakin mutane biyar aka gano a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, bayan wasu yan ta’adda sun kaddamar da sabon hari a kan al’ummar karamar hukumar Guma da ke jihar Benue.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutane 10 sun bata yayin da aka tura wata tawaga domin kakkabe dazuzzuka tare da binciko inda suke.

Shugaban karamar hukumar Guma, Caleb Aba, a wata hira ta wayar tarho ya bayyana cewa lamarin ya afku ne a yammacin ranar Litinin a garin Mbagwen amma an sanar masa a ranar Talata da rana.

Kara karanta wannan

Katsina: Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Sun Kashe Mutum 3, Sun Tafi Da Matar Aure

Asali: Legit.ng

Online view pixel