Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan Ekiti

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan Ekiti

Ɗan takarar jam'iyyar All Progressive Congress APC, Mista Biodun Oyebanji, ya lashe zaɓen gwamnan jihar Ekiti wanda ya gudana ranar 18 ga watan Yuni, 2022.

Da yake ayyana wanda ya samu nasara, baturen zaɓe na hukumar INEC, Farfesa Oyebode Adebowale, ya ce Oyebanji ya samu kuri'u 187,057 da suka ba shi damar zama zakara a zaɓen.

Ya ce Obebanji ya cika duk wasu sharuɗɗa da doka ta tanada kuma saboda haka shi ne zaɓaɓɓe, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Biodun Oyebanji.
Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan Ekiti Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce:

"Ni, Farfesa Oyebode Adebowale, halastaccen baturen zaɓen gwamnan jihar Ekiti 2022 wanda ya gudana ranar 18 ga watan Yuni, Biodun Oyebanji, ɗan takarar APC bayan cika dukkan sharuɗɗa, Na ayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara."

Kara karanta wannan

2023: 'Ka ci amanar mu' Gwamna Okowa da Atiku ya zaɓa mataimaki ya shiga tsaka mai wuya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa 5 game da rayuwar Oyebanji, wanda ya zama zabaɓɓen gwamnan Ekiti.

1. Haihuwa

Biodun Abayomi Oyebanji, wanda ya fi shahara da BAO fitaccen ɗan siyasa ne kuma mamba a jam'iyyar APC, an haife shi ranar 21 ga watan Disamba, 1967 a garin Ikogosi-Ekiti, jihar Ekiti.

2. Ilimi

Oyebanji ya samu shaidar kammala karatun digirinsa na farko a fannin kimiyyar siyasa (BSc Political Science) a 1989 daga jami'ar jihar Ondo wacce a yanzu ta koma jami'ar jihar Ekiti, Ado-Ekiti.

3. Tsohon Malamin Jami'a

Oyebanji ya fara aiki ne a matsayin Malamin Jami'a a tsangayar koyar da ilimin kimiyyar siyasa, Jami'ar jihar Ekiti, inda ya yi aiki na tsawon shekara huɗu (1993 –1997).

Daga nan wuce ya rike mukamanin Manaja ɓangaren ajiya da harkokin kuɗi a Bankin Omega wanda yanzun ya koma Heritage Bank har zuwa watan Mayu, 1999.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu ya gaje Babban Ofishin yaƙin neman zaɓen shugaba Buhari a Abuja

4. Tsohon Sakataren gwamnatin jihar Ekiti

Har zuwa lokacin da ya yanke shawarin neman kujerar gwamna, Oyebanji, shi ne Sakataren gwamnatin Ekiti ƙarƙashin gwamna mai ci, Kayode Fayemi.

5. Iyali

Zababben gwamnan yana da mata ɗaya, Misis Oyebanjo, Gimbiyar Ado Ekiti kuma ta kusa zama Farfesa a Jami'ar Ibadan, jihar Oyo.

A wani labarin kuma Wani mutumi ya fara tattaki da ƙafa daga Bauchi zuwa Legas don kaunar Tinubu a 2023

Yayin da gangar siyasa ke cigaba da kaɗawa mutane na kokarin nuna goyon bayan su ga ƴan takara ta hanya daban-daban.

Wani mai suna Usman Adamu ya isa Kafanchan dake Kaduna, ya taso daga Bauchi zuwa Legas don nuna kaunarsa ga takarar Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel