'Ka ci amanar yardar da muka maka' shugabannin kudu, arewa sun caccaki mataimakin Atiku

'Ka ci amanar yardar da muka maka' shugabannin kudu, arewa sun caccaki mataimakin Atiku

  • Shugabannin kudancin Najeriya sun yi watsi da matsayin mataimakin da aka ba gwamna Okowa na jihar Delta
  • A wata sanar da shugaban kungiyoyin suka fitar, sun bayyana cewa Okowa wanda aka cimma matsayi a jiharsa ya ci amana
  • Ɗan takara PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya zabi gwamnan ya zama abokin tarakararsa kuma tuni PDP ta tantance shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gamayyar Ƙungiiyoyin dattawan kudu da tsakiyar Najeriya (SMBLF) sun fusata da gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, bisa amincewa da matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ga Atiku Abubakar a zaɓen 2023 da ke tafe.

Sun bayyana haka ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban SMBLF/PANDEF, shugaban kungiyar yarbawa Afenifere, Chief Ayo Adebanjo, shugaban ƙungiyar arewa ta tsakiya, Pogu Bitrus, shugaban Inyamurai, Ohaneze Indigbo, Farfesa George Obiozor.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Okowa ya cancanci zama mataimakin Atiku, PDP ta fitar da sakamakon tantancewa

Gwamna Okowa na jihar Delta.
'Ka ci amanar yardar da muka maka' shugabannin kudu, arewa sun caccaki mataimakin Atiku Hoto: Vanguardngr.com
Asali: UGC

A sanarwan, sun ce abun damuwane da cin amana gwamna Okowa, wanda ke jagorantar ƙungiyar gwamnonin Kudu kuma ɗan asalin Owa-Alero, ƙaramar hukumar Ika North-East (yankin dake da yawan Ibo) ya karɓi wannan matsayin.

Vanguard ta ruwaito wani sashin sanarwan ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A baya gwamnoni 17 na kudancin Najeriya na PDP da APC karkashin gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, sun gana a Asaba, jihar Delta, inda suka cimma matsaya kan mulki ya koma kudu bayan kammala wa'adin Buhari kuma Okowa ne ya karɓi baƙuncin taron."
"Mun yaba da matsayar gwamnonn domin sun nuna wakilan al'umma ne su, inda muka bi sahu kuma muka fitar da sanarwa bayan taron da muka yi a Abuja a watan Agusta, muka bukaci mulki ya koma kudu."

Bayan haka SMBLF ta ƙara da cewa sun gargaɗi kowane mutum daga yankin kudu, tsofaffin gwaamnoni, Sanatoci, da sauran masu ruwa da tsaki kada su amince a ba su mataimakin ɗan takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Ana gab da zaɓe, Tsohon Kwamishina da wasu jiga-jigan APC makusantan Ministan Buhari sun koma PDP

Gwamna Okowa ya ci amanar yardar da muka masa

A sanarwan shugabannin sun ce matakin Okowa na karɓan mataimakin ɗan takara ya ci amanar yardar da takwarorin gwamnonin kudu suka masa, da sauran mutanen kudancin Najeriya.

"Abun takaici da bakin ciki shi ne gwamna Okowa na Delta, wand a ya fi kowa sanin wannan matsayar ya amince da nadinsa mataimaki ga Atiku Abubakar, bamu da matsala da Okowa amma abin da ya aikata ya bamu kunya."
"Saboda haka mun yi watsi da gwamna Okowa da matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, mun barshi da matsayin amma ya kamata duniya ta sani ya ci amanar mu."

A wani labarin kuma PDP na tsaka da kokarin zaɓo mataimakin Atiku, Sanata mai ci ya sauya sheƙa zuwa APC a hukumance

Sanata mai wakiltar kudancin jihar Oyo, Sanata Kola Balogun, ya tabbatar da sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC a hukumance.

Kara karanta wannan

Muna bukatar PDP ta koma mulki a 2023: Abokin tafiyar Atiku ya lashi takobi

Sanatan ya aike da wasikar matakin da ya ɗauka ga shugaban majalisar dattawa kuma ya karanta a zaman su na ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel