Allah Bai Manta Dani Ba: Bidiyon Budurwa Mai Shekaru 52 da Tayi Auren Farko

Allah Bai Manta Dani Ba: Bidiyon Budurwa Mai Shekaru 52 da Tayi Auren Farko

  • Wata mata mai shekaru 52 ta shige sahun ma'aurata tare da fita daga sahun gwauraye yayin da daga karshe ta amarce da masoyinta
  • Sabuwar amaryar ta kasa boye irin tsananin farin cikin da take ciki tare da godiya ga Ubangiji da ya tabbatar da hakan, inda ta ce burinta ya cika
  • An wallafa bidiyon ranar bikinta a shafukan sada zumuntar zamani na TikTok wanda tun daga lokacin ya fara yawo

Bayan kwashe tsawon shekaru tana jira, wata mata 'yar Najeriya mai shekaru 52 ta hadu da abokin rayuwarta kuma sun shige daga ciki.

Wata mai amfani da shafin TikTok mai suna Ogechi Gideon Udofia ta wallafa bidiyon wata mata cikin rigar bikinta a ranar aurenta tare da shawartar masu amfani da yanar gizo da cewa lokacin Ubangiji shi ne daidai.

Kara karanta wannan

Fasto ta Bayyana Bidiyon Jinjira da aka Haifa da Sunan Allah a Kunnuwanta a Cocinta

Allah Bai Manta Dani Ba: Bidiyon Budurwa Mai Shekaru 52 da Tayi Auren Farko
Allah Bai Manta Dani Ba: Bidiyon Budurwa Mai Shekaru 52 da Tayi Auren Farko. Hoto daga @o.gbest
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta ce burinta ya cika

A wani bidiyo, an ga amaryar na bayyana yadda take ji a kan yadda daga karshe tayi aure.

Matar mai cike da farinciki ta ce ji take kamar ta ruga da gudu, tare da zaro idanuwanta gami da cewa Ubangiji ya yi nasa ikon.

A cewarta:

"Yau rana ta ce. Ina matukar murna. Buri na ya cika. Ji nake kamar in ruga da gudu. Ubangiji ya yi nasa ikon. Ina cikin farin ciki."

Jama'a sun yi mata addu'o'i

Babu jimawa jama'a suka yi caa inda suka dinga kwarara mata addu'o'in fatan alheri.

Flora Abraham675 ta ce:

"Kai gaskiya ina taya ki murna, Ubangiji zai baka mamaki ta yadda ba za ka iya misalta farincikin da za ka shiga ba. Nan da watanni 9 za mu taya ki murna saboda babu abun da ya gagari Ubangiji."

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

Queen Amina ta ce: "Ina taya ki murna, ina fatan za ki samu cikakken farin ciki da fatan gidanki zai zama cikin wadanda suka fi kowa farinciki Amin."
richloretta ta ce: "Kai wannan wata kalmace da na gani a cocina, gaskiya kin yi matukar kyau."

Angel ta ce:

"Gaskiya ina taya ki murna, Na shafi tabaraki daga muwafakar da Ubangiji ya miki, na yarda Ubangiji ne ke da lokaci, Ubangiji ya albarkaci wannan auren naku."

Budurwa mai shekaru 24 ta aura jakar da ta yi soyayya da ita na shekaru 5

A wani labari na daban, wata mata ta bayyana yadda ta fada kogin soyayya da wata jaka, kuma har ta kai ga auren jakar. Rain Gordon ta ce kullum soyayyar jakar tana ratsa zuciyarta kuma hakan ya girma ya koma sha'awa.

A watan Yunin wannan shekarar ne ta bayyana aurenta da jakar, wacce ta sanya wa suna Gideon.

Kara karanta wannan

Dan Dora Akunyili: Fastoci Sun Rika Tatsar Kudin Mahaifiyana Da Sunan Za Su Yi Mata Maganin Cutar Kansa

Matar mai shekaru 24 ta ce duk da a baya tayi soyayya da samari da dama, amma tafi jindadin soyayya da abubuwa marasa rai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel