Budurwa mai shekaru 24 ta aura jakar da ta yi soyayya da ita na shekaru 5
- Kowa da kiwon da ya karbesa, makwabcin mai akuya ya siya kura
- Wata mata ta fada kogin soyayya da wata jaka, har ta auri jakar
- An daura auren matar mai shekaru 24 da jakar a watan Yunin wannan shekarar
Wata mata ta bayyana yadda ta fada kogin soyayya da wata jaka, kuma har ta kai ga auren jakar. Rain Gordon ta ce kullum soyayyar jakar tana ratsa zuciyarta kuma hakan ya girma ya koma sha'awa.
A watan Yunin wannan shekarar ne ta bayyana aurenta da jakar, wacce ta sanya wa suna Gideon.
Matar mai shekaru 24 ta ce duk da a baya tayi soyayya da samari da dama, amma tafi jindadin soyayya da abubuwa marasa rai.
KU KARANTA: Yadda 'yan sanda suka dinga yi wa mutumin da aka sace wa mota dariya
Matar ta fara ganin mijin nata, a watan Augustan 2015, bayan ta je wani shago siyayya. Ta ce tana ganin jakar ta ji ta fara sonta.
Ta ce soyayyarsu ta yi kamari a watan Nuwamban 2015, kafin ta auri jakar a watan Yunin shekarar nan.
Kamar yadda tace, "Tun ina yarinya na yarda cewa komai yana da rai. Tun ina yarinya nake fadawa soyayya da wurare, kamar sababbin wuraren siyayya a garinmu, amma na san ba daidai bane, shiyasa ban taba fada wa kowa ba."
KU KARANTA: 'Yan sanda sun sake damke mutumin da yayi bidiyon da ya tada zanga-zangar EndSARS
A cewarta, "Ban taba sanin cewa za mu kare da Gideon a matsayin miji da mata ba. Don zan iya in zauna in yi ta kallonshi, ina hira da shi na tsawon sa'o'i, amma hirar zuciya da zuciya."
"Gideon miji ne a gareni, aboki kuma wanda nake koyon darasi a wurinsa. Gani nake yi kamar ya fi ni sanin kaina," a cewarta.
A wani labari na daban, wata mata 'yar kasar Jamus, mai suna Renate Wedel, ta mutu a watan Disamban 2019 tana da shekaru 81 a duniya, ta barwa makwabtanta gado mai dumbin yawa.
Tun a shekarar 1975 aka yi kiyasin tana da dukiya mai kimar $7,500,000, wanda yayi daidai da N2,861,250,000. Matar, wacce ta zauna da marigayin mijinta, Alfred Wedel, a Waldsolms, tsakiyar Jamus.
Dama anguwar Waldsolm tana da kauyaku 6 a karkashinta. Bankuna sun yi ta kiran shugaban anguwar, suna sanar dashi batun zunzurutun dukiyar da ta bari.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng