Wasu ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar ‘dan takaran Sanatan Kano cikin dare
- Labari na zuwa cewa ana zargin ‘yan Bindiga sun sace tsohuwar AA Zaura a gidan ta da tsakar dare
- An dauke wannan dattijuwa ne dazu a kauyen Zaura da ke karamar hukumar Ungogo a birnin Kano
- Shugaban karamar hukumar Ungogo, Abdullahi Garba Ramat da ‘yan sanda sun tabbatar da lamarin
Kano - Wasu miyagu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun dauke tsohuwar Abdulkarim Abdulsalam Zaura wanda aka fi sani da A. A Zaura.
Rahoton da mu ka samu daga Solacebase a safiyar Litinin, 6 ga watan Yuni 2022, ya tabbatar mana da wannan labarin maras dadi.
Abdulkarim Abdulsalam Zaura shi ne ya lashe zaben fitar da gwani na zama Sanatan jihar Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC.
An yi awon gaba da Hajia Laure Mai Kunu ne cikin tsakar daren Litinin, kafin a kira sallar asuba.
Shugaban karamar hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya bayyanawa jaridar wannan, ya ce sun sanar da jami’an tsaro.
‘Yan bindigan sun dauke wannan Baiwar Allah mai yawon shekaru a unguwar Rangaza da ke cikin kauyen Zaura a karkashin Ungogo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Puff Adder sun shiga bakin aiki
Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya shaida cewa sun tura dakarun Puff Adder zuwa wannan yanki.
SP Abdullahi Kiyawa ya na sa ran rundunar ‘yan sandan jihar su iya ceto wannan Baiwar Allah, sannan su damke wadanda suka dauke ta.
Abdullahi Garba Ramat ya yi magana
Rahoton da ya fito daga Sahelian Times dazu, ya nuna Abdullahi Garba Ramat ya tabbatar da aukuwar abin ne a shafin sada zumunta.
“Innalillahi wa inna’ilaihirraj’un, a yau mun tashi da mummunan labarin cewa a safiyar yau Litinin wasu ƴan bindiga sun yiwa ƙaramar hukumar Ungogo dirar mikiya inda su ka yi awon gaba da mahaifiyar A. A Zaura zuwa wani guri da ba a sani ba.
Allah ka kubutar mana da Baba Laure”
Legit.ng Hausa ta samu labari kwanakin baya wasu sun dauke mahaifiyar ‘dan majalisar dokoki, Hon. Isyaku Ali a karamar hukumar Gezawa.
An yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa
A baya an ji labari, ‘dan majalisar jihar Osun, Hon. Bamidele Salam ya nemi gwamnati ta ba dangin matafiyan jirgin kasan Abuja-Kaduna hakuri.
‘Dan majalisan ya zargi gwamnati da nuna rashin damuwa wajen ceto wadannan mutane da aka dauke a jirgin kasa fiye da watanni biyu da suka wuce.
Asali: Legit.ng