ISWAP Ta Kashe Babban Kwamandan Boko Haram, Ummate Ma, Da Sojoji Ke Nema Ruwa A Jallo

ISWAP Ta Kashe Babban Kwamandan Boko Haram, Ummate Ma, Da Sojoji Ke Nema Ruwa A Jallo

  • Rikicin da ya barke tsakanin Boko Haram da ISWAP ya yi sanadin kashe babban kwamandan Boko Haram, Ummate Ma, da wasu dakarunsa da dama
  • Rahotanni sun nuna cewa ISWAP ta kai wa tawagar Ummate Ma hari ne a Dutsen Mandara ta bude masa wuta ta kuma kwace makamai da babura daga mayakansa
  • Bayanai na sirri suna nuna cewa ISWAP ta kai wa tawagar Ummate Ma harin ne a matsayin martani kan kashe kwamandansu Abou Sadiqou da mayakansa

Mummunan rikici ya kaure tsakanin kungiyar ta'addanci ta ISWAP da Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, Boko Haram, wacce ta yi sanadin kashe hatsabibin kwamanda mai suna Ummate Ma, da mayakansa, rahoton Leadership.

An tattaro cewa Ummate Ma, wanda aka fi sani da Muhamma wanda ke da mukamin Khayd (Gwamna) da mayakansa, an kashe su ne a ranar 1 ga watan Yuni lokacin da mayakan ISWAP suka kai wa tawagar Kwamandan hari a Dutsen Mandara a karamar hukumar Gwoza a hanyarsa ta zuwa Kamaru.

Kara karanta wannan

Dakarun MNJTF Sun Kashe 'Yan Boko Haram Da ISWAP 805 Da 'Yan Bindiga 5 a Benue

ISWAP Ta Kashe Babban Kwamandan Boko Haram, Ummate Ma, Da Sojoji Ke Nema Ruwa A Jallo
Ummate Ma: ISWAP Ta Kashe Babban Kwamandan Boko Haram Da Sojoji Ke Nema Ruwa A Jallo. Hoto: @LeadershipNGR
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar bayanan sirri da Zagazola Makama, Kwararre kan tsaro da yaki da ta'addanci a Tafkin Chadi ya samu daga majiyar sojoji, wacce Leadership ta samu, harin ya yi sanadin musayar wuta na tsawon awa biyu tare da kashe yan Boko Haram da dama.

Majiyar ta ce:

"Yan ta'addan ISWAP din da suka taso daga kauyukan Cinana Gwoshe, Barawa da Agaba a motocci da babura sun ci galaba kan yan Boko Haram, suka kashe da dama cikinsu tare da kwace makamansu, babura da motocci masu bindiga."

Majiyar ta ce an harbi kwamandan da bindiga a kirjinsa da wasu sassan jikinsa.

Abin da yasa ISWAP ta kai wa Boko Haram harin

An rahoto cewa ISWAP ta kai harin ne a matsayin martani kan kashe babban kwamandan ISWAP, Abou Sadiqou da wasu yan ta'adda da dama da Boko Haram ta yi a kusa da Dutsen Mandara.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC

Majiyar ta kara da cewa yan ta'addan da farko sun dakatar da kai wa sojojin Najeriya manyan hare-hare sun mayar da hankali kan yaki da abokan hammayarsu, sun sha alwashin sai sun ga bayansu.

Ummate Ma wanda aka fi sani da Muhamma shine na 217 a jerin yan ta'adda da Rundunar Sojojin Najeriya ke nema ruwa a jallo.

Ya shiga Boko Haram, tsagin Abubakar Shekau a 2009, har ya samu karin girma zuwa gwamna.

Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla fararen hula uku ne suka riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai hari a kauye da ke karamar hukumar Chibok a Jihar Borno da yammacin ranar Jumma'a.

Kungiyar yan ta'addan sun afka kauyen Kautikari da ke kusa da gari Chibok misalin karfe 4 na yamma, suna harbe-harbe ba kakkautawa kuma suka kona gidaje da dama a cewar majiyoyi na tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An kuma: Mummunan fashewa ta auku a Kano an rasa shaguna, mutum 20 sun jikkata

A cewar majiyar, maharan sun iso ne a cikin motocci guda biyar dauke da bindiga mai harbo jiragen yaki kuma suka shigo cikin sauki ba tare da an nemi taka musu birki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel