Gwamnatin El-Rufai za ta kirkiri ‘Film Village’ domin matasa su samu sana’a a Kaduna

Gwamnatin El-Rufai za ta kirkiri ‘Film Village’ domin matasa su samu sana’a a Kaduna

KADIPA mai kwadaito masu zuba hannun jari a Kaduna za ta gina kauyen shirya wasan kwaikwayo

Shugaban hukumar, Khalil Nur Khalil ya hadu da Shugaban Fasaha Café da Rahma Sadau a kan hakan

Wannan aiki zai taimakwa matasa wajen samun ayyukan yi, za kuma a kware wajen shirya fina-finai

https://twitter.com/InvestKaduna/status/1532284440226963456?t=5DW8jpCC1UzEUO1KyVt5Hw&s=19

Kaduna - Babban sakataren hukumar KADIPA na jihar Kaduna, Khalil Nur Khalil ya cigaba da kokarin ganin an gina kauyen shirya wasan kwaikwayo.

A wani jawabi da ya fito daga shafin KADIPA a dandalin Twitter a ranar Alhamis, an fahimci gwamnatin Kaduna tana nan a kan aikin ‘Film Village’.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Wasu Makusanta da Mukarraban Shugaban kasa 7 da suka gagara samun takara a APC

Khalil Nur Khalil ya hadu da wakilan KCTA, shugabar Fasaha Café, Joseph Ike, da fitacciyar ‘yar wasar kwaikwayo, Rahma Sadau a kan wannan shirin.

Shugaban na KADIPA ya yi wannan zama ne da nufin ganin yadda a za a iya gina kauyen shirya wasan kwaikwayo da zai bunkasa tattalina arzikin kasa.

Kamar yadda sanarwar ta nuna, aikin zai taimaka wajen kafa Kaduna Film Village a hukumance domin sa ido a kan harkokin wasan kwaikwayo a Kaduna.

Gina Film Village a Rigachikun

Haka zalika ana neman gina wannan kauye a filin kasuwar baja-kolin Duniya a Rigachikun, ana sa rai wannan zai jawo kwarararrun ‘yan wasan kwaikwayo.

Gwamnatin El-Rufai za ta kirkiri ‘Film Village'
Khalil Nur Khalil, Joseph Ike, da Rahma Sadau Hoto: @InvestKaduna
Asali: Twitter

malAkwai taurari a garuruwan Legas, Capetown, Accra da Dubai da za ayi amfani da su wajen horas da kananan yara masu tasowa domin su kware a harkar fim.

Wani aiki da KADIPA ta ke son yi shi ne shirya bikin wasan ‘yan fim da marubutan wasan kwaikwayo na gida domin su hada-kai da na taurarin Duniya.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya shiga tsakanin shugabannin PDP bayan Atiku ya lashe tikitin takarar shugaban kasa

Za a daina zaman banza

A karshe kuma shugaban hukumar zai tallata wannan aiki da nufin samun masu hannun jarin da za su narka dukiyarsu domin a kirkiri dinbin ayyukan yi a jihar.

Muddin aka ci nasara wajen wannan aiki, matasa da-dama za su samu abin yi, su daina zaman banza.

Shekarun baya gwamnatin tarayya ta taba kawo shawarar yin irin wannan aiki a jihar Kano, amma wasu su ka nuna cewa hakan zai iya jawo lalacewar tarbiya.

AA Zaura zai gina Film Village

A zaben 2019 an ji fitaccen dan siyasar nan, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim watau A.A. Zaura ya dauki alkawarin gina wurin shirya fina-finai idan ya zama Gwamna.

Mai neman kujerar gwamnan a Kano, ya taba sa gasar bidiyon rera waka, inda aka ji za a ba wasu mutane kyaututtuka da suka hada da mota, keke napep da babur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel