Tashin Hankali: Ƴan Ta'adda Sun Bindige Ango Har Lahira, Sun Sace Amaryarsa Mai Juna Biyu a Kaduna

Tashin Hankali: Ƴan Ta'adda Sun Bindige Ango Har Lahira, Sun Sace Amaryarsa Mai Juna Biyu a Kaduna

  • Yan bindiga kimanin su 50 sun kai hari garin Jere a Kaduna inda suka kashe wani ango yayin da ya yi kokarin hana su tafiyar da amaryarsa mai juna biyu
  • Yan bindigan sun kuma sace matar tsohon kwamishinan rage talauci na Kaduna, Abdulraham Ibrahim Jere, da yarsa, da kanwarsa da yar uwar matarsa
  • Wani mazaunin garin ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce matasa sun fusata domin yan bindiga sun shafe kimanin awa uku suna garin ba tare a jami'an tsaro sun zo ba

Kaduna - Wasu yan bindiga sun bindige wani ango har lahira sannan suka sace amaryarsa mai dauke da juna biyu a garin Jere da ke karamar hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.

Yan bindigan sun kuma sace mutane hudu a gidan tsohon kwamishinan Rage radadin talauci na Jihar Kaduna, Abdulrahman Ibrahim Jere, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yadda aka tsinci gawarwakin wani dan kasuwa, matarsa da yaransu 3 baje a gidansu

Tashin Hankali: Ƴan Ta'adda Sun Bindige Ango Har Lahira, Sun Sace Amaryarsa Mai Juna Biyu a Kaduna
'Yan Bindiga Sun Harbe Ango Har Lahira, Sun Sace Amaryarsa Mai Juna Biyu a Kaduna. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindiga kimanin 50 ne suka isa Jere, wani gari da ke kan babban hanyar Kaduna zuwa Abuja. An ce sun rika bi gida-gida amma da alama gidan tsohon kwamishinan, Abdulraham Ibrahim Jere ne ainihin inda suke son zuwa amma baya gari.

Sai dai, sun sace matarsa da yarsa, kanwarsa da yar uwar matarsa.

Hassan Adamu Jere, wani mazaunin garin ya ce, yan bindigan sun kuma kai hari gidan wani ango suka yi yunkurin sace amaryar amma angon bai yarda ba.

Ya ce yayin gardama da su, sun bindige angon har lahira.

Matasan garin Jere sun nuna bacin ransu game da harin, sun yi barazanar yin korafi kan jami'an tsaro

Ya ce matasan garin sun fusata kan yadda yan bindigan ke kawo hari duk da jami'an tsaro da aka girke a garin yan bindigan sun shafe awa uku suna cin karensu babu babbaka.

Kara karanta wannan

Miyagun Yan bindiga kan 'Babura sama da 200' sun kai wani mummunan hari jihar Katsina

"Mun yi ta kiran jami'an tsaro a waya amma ba su kula mu ba. Wannan shine babban hari na biyu a garin mu cikin watanni uku kuma muna garin jami'an tsaron da aka girke a garin ba su da amfani a wurin mu," wani fusataccen matashi, Adamu Jere, ya ce.

Ibrahim Salisu, wani mazaunin garin, ya za su shigar da karar jami'an tsaron da ke Jere, ya kara da cewa abin da suke yi ya nuna 'suna hada baki da yan bindigan ko kuma ba su damu da tsaron mutane ba.'

Ya ce awanni bayan yan bindigan sun tsere, jami'an tsaron sun yi kokarin bin sahunsu kuma daga bisani sun sanar da mutanen garin cewa sun kashe biyu cikin yan bindigan.

Kakakin yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai amsa kirar da aka masa ba na neman karin bayani kan lamarin a lokacin hada wannan rahoto.

Jaridar Legit.ng Hausa ta samu karin bayani daga matashi mazaunin garin na Jere game da afkuwar harin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe ango, sun sace wasu da dama harda iyalan tsohon kwamishina a Kaduna

Matashin wanda ya bukaci kada a ambaci sunansa ya ce:

"Tabbas abin ya faru a garin Jere misalin karfe 10 na dare. Sun yi kokarin tafiya da wani abokin aiki na amma ya sha da kyar daga hannunsu," in ji shi.

Ya kuma yi addu'ar Allah ya kubutar da wadanda aka sace din sannan shi kuma wanda aka kashe Allah ya jikansa da rahama. Amin.

Daga karshe ya mika rokonsa ga hukumomin tsaro da su kara zage damtse domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al'ummar garin da ma kasa baki daya.

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel