Rashin tsaro: Mutane 13000 daga kauyen Katsina sun tsere zuwa Nijar inji Gwamna Masari

Rashin tsaro: Mutane 13000 daga kauyen Katsina sun tsere zuwa Nijar inji Gwamna Masari

  • Akwai akalla Katsinawa 13,500 da sun koma zama a Jamhuriyyar Nijar a dalilin ta’adin ‘yan bindiga
  • Gwamna Aminu Bello Masari ya ce al’ummar Jihar Katsina sun shiga masifa a wasu kauyuka 13
  • Kauyukan da suke kusa da dajin rugu su na fuskantar ta’adin ‘yan bindiga babu dare-babu rana

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce al’ummarsa sun sha matukar wahala a dalilin ta’adin miyagun ‘yan bindigan da suka hana sakat.

Jaridar Premium Times ta rahoto Mai girma Aminu Bello Masari yana cewa fiye da mutum 13, 000 da ke jihar ta Katsina sun tsallaka zuwa Jamhuriyyar Nijar.

Kasar Jamhuriyyar Nijar ta na kan iyaka da Najeriya ta jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.

A ‘yan shekarun nan, jihar ta Katsina (mahaifar Muhammadu Buhari) da wasu yankunan Arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Ƴan Boko Haram Da ISWAP Sun Yada Zango a Ƙananan Hukumomi 2 a Kaduna

‘Yan bindiga su kan yi garkuwa da mutane, su kona garuruwa, sannan kuma su sace kayan al’umma ko su kona kauyukan ba tare da an taka masu burki ba.

Da yake jawabi a yammacin ranar Lahadi, an rahoto Aminu Masari yana fadawa Kayode Fayemi cewa kauyukan da ke kusa da dajin Rugu su na ganin ha’ula’i.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Masari
Gwamna Rt. Hon. Aminu Bello Masari da Kayode Fayemi Hoto: kfayemi
Asali: Twitter

Dr. Kayode Fayemi yana kamfe

Dr. Kayode Fayemi ya ziyarci jihar ne domin neman goyon bayan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa da ake shirin yi kwanan nan.

Zuwa yanzu Kayode Fayemi yana cikin masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a APC.

Halin da ake ciki a Katsina

Kamar yadda Gwamnan ya ke fada, garuruwa kusan 13 da ke kan iyaka da dajin na Rugu wanda ya yi iyaka da jihohin Kaduna da Zamfara sun yi gudun hijira.

Kara karanta wannan

‘Dan takaran NNPP da ya bi Ganduje, ya janye jiki ya dawo Kwankwasiyya bayan awa 24

Yayin da wasu suka koma kauyukan da ke kusa da su, har ta kai wasu sun shiga kasar Nijar. Wadannan Bayin Allah sun rasa hanyar da suke samun abincinsu.

A halin yanzu gwamnatin Katsina ta na kashe N100m wajen farfado da kauyen Shinfida da aka kona kurmus, mazauna 13, 5000 na kauyen su na zaune a kasar Nijar.

Babba Kaita zai yi takara

Dazu kun ji labari Sanata Ahmed Babba Kaita ya samu nasara a zaben zama ‘dan takarar jam’iyyar PDP na ‘dan majalisar dattawa na Arewacin Katsina.

Wannan karo ‘Dan majalisar zai tsaya neman kujerar ne a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP. A watan Afrilun da ya gabata Sanatan ya sauya-sheka daga APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel