Ana buga kugen zaben 2023: EFCC ta kara gurfanar da fitattun 'yan siyasa 5 kan zargin wawurar N23.3b

Ana buga kugen zaben 2023: EFCC ta kara gurfanar da fitattun 'yan siyasa 5 kan zargin wawurar N23.3b

  • Hukumar EFCC ta sake gurfanar da Sambo Dasuli, Attahiru Bafarawa, Bashir Yuguda da wasu mutum biyu kan zargin satar N23.3 biliyan
  • Ana zarginsu da laifuka 25 da suka hada da damfara tare da watanda da kudin makamai inda suka yi kamfen din siyasa da kudaden
  • A halin yanzu an bayar da belinsu cike da tsohon sharadin belin da suka mora a baya inda za acigaba da shari'ar a watan Yuni

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, a ranar Litinin ta sake gurfanarwa da Kanal Sambo Dasuki, tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa, tsohon ministan kudi, Bashir Yuguda da wasu mutum biyu kan zargin waddaka da zunzurutun kudin kasa har N23.3 biliyan.

Sauran da aka gurfanar tare da su sune 'dan Bafarawa, Sagir da kamfaninsu mai suna Dalhatu Investment Limited, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

An gurfanar da su ne kan zargin laifuka 25 da suka hada da waddaka da kudin kasa tare da da samun kudin ta hanyar damfara.

Ana buga kugen zaben 2023: EFCC za ta kara gurfanar da fitattun 'yan siyasa 5 kan zargin wawurar N23.3b
Ana buga kugen zaben 2023: EFCC za ta kara gurfanar da fitattun 'yan siyasa 5 kan zargin wawurar N23.3b. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Wadanda ake zargin an fara gurfanar da su a shekarar 2015 a gaban Alkali Peter Affen wanda yanzu alkali ne a kotun daukaka kara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga bisani an sake gurfanar da su a gaban Alkali Husseini Baba Yusuf, wanda yanzu shi ne babban alkalin babban birnin tarayya a Abuja. Sun gurfana a gaban Alkali Yusuf Halilu.

EFCC tana zarginsu da waskar da kudi daga ofishin mai bada shawara kan tsaron kasa tsakanin 2013 zuwa 2015 inda suka salwantar da su wurin gangamin kamfen din zabe.

Wadanda ake zargin suna morar beli amma cike da sharuddan belin baya da aka gindaya musu.

Halilu ya dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Yuni da 7 ga watan Yuni domin sauraron shari'ar.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Shugaban karamar hukumar Keffi da aka sace ya samu yanci

Tun a baya, Lateef Fagbemi, SAN, lauyan Bafarawa ya yi kira ga kotun da ta bar wadanda ake kara su mori beli da sharuddan da aka gindaya musu a baya.

Ya ce a ranar 21 ga watan Disamban 2015, Alkali Affen ya bayar da belinsu kuma Baba-Yusuf a ranar 7 ga watan Oktoban 2016 ya bukaci su cigaba da amfani da sharuddan belin.

EFCC ta gurfanar da Dasuki, Yuguda da Bafarwa gaban ƙuliya manta sabo

A wani labari na daban, hukumar yaki zamba da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gurfanar da mai baiwa tsohon shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro kanal Sambo Dasuki tare da tsohon gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa da wasu mutane hudu gaban kotu kan zarginsu da hada kai wajen karkatar da kudi naira biliyan 19.

EFCC ta gurfanar da Dasuki, da Bafarawa ne gaban babban kotun tarayya dake Abuja tare tsohon ministan kudi Bashir Yuguda, tsohon daraktan kudi na ofishin Dasuki, Shuaibu Salisu tare da ɗan Bafarawa da kuma kamfanin Bafarawa mai suna Dalhatu Ivestment Limited.

Kara karanta wannan

Jihar Bauchi: Gwamna ya yi martani kan zagin Annabi da wata mata ta yi

Asali: Legit.ng

Online view pixel