Sai bayan baka ake: Muhimman dalilai guda 7 da sanya soyayyar Murtala a zukatan yan Najeriya

Sai bayan baka ake: Muhimman dalilai guda 7 da sanya soyayyar Murtala a zukatan yan Najeriya

A ranar Litinin, 13 ga watan Feburairu ne marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja, janar Murtala Muhammed ya cika shekaru 42 da biyu mutuwarsa, tun bayan da Sojojin tawaye suka bindige shi a Legas.

Sai dai duk da shekarun da janar Murtala ya kwashe a kushewa, amma yan Najeriya na cigaba da bayyana shauki tare da soyayyarsu game da shi, wannan ne abinda ya daure ma jama’a kai, kuma yasa VOA hausa ta tuntubi wani masanin tarihi, Ado Kurawa.

KU KARANTA: Yan Hisbah sun kai samame, sun damke mabarata guda 8 a cikin garin Kano

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin muhimman ayyukan da Muratala ya yi da suka sanya soyayarsa a zukatan yan Najeriya akwai:

Sai bayan baka ake: Muhimman dalilai guda 6 da sanya soyayyar Murtala a zukatan yan Najeriya
Murtala

- Kafa tubulin sabuwar kundin tsarin mulki

- Samar da sabuwar babban birnin tarayya a Abuja

- Kirkirar sabon tsarin mulki na Najeriya

- Daura tubalin samar da jam’iyyu masu rassa a dukkanin Najeriya

- Aika ma’aikata zuwa bangarori daban daban

- Yaki da cin hanci da rashawa

- Kirkiran jihohi guda 7, da suka hada da Bauchi, Benue, Borno, Imo, Niger, Ogun da Ondo

Bugu da kari, dukkanin nasarorin nan da Murtala ya samu ya same su ne cikin kwanaki 200 da yayi yana mulkar Najeriya, tare da mataimakinsa Olusegun Obasanjo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng