Yanzun nan: Shugaban karamar hukumar Keffi da aka sace ya samu yanci

Yanzun nan: Shugaban karamar hukumar Keffi da aka sace ya samu yanci

  • Shugaban karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa, Muhammad Shehu-Baba da hadimisa, Tanimu Mohammed da yan bindiga suka sace sun samu yanci
  • Yan bindigar sun sako Shehu-Baba da hadimin nasa ne a daren ranar Asabar, 21 ga watan Mayu, da misalin karfe 9:oo na dare
  • Rundunar yan sandan jihar Nasarawa da ta tabbatar da hakan, ta ce an kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin

Nasarawa - Yan bindiga sun saki shugaban karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa, Muhammad Shehu-Baba da hadimisa, Tanimu Mohammed, da suka yi garkuwa da su.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, Ramhan Nansel, ya tabbatar da sakin nasu ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Lahadi, 22 ga watan Mayu, a garin Lafia.

Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar na Keffi tare da hadimin nasa a hanyar Keffi-Akwanga a ranar Juma’a bayan sun kashe wani jami’in dan sanda da ke tare da shi, Alhassan Habib.

Kara karanta wannan

Jihar Bauchi: Gwamna ya yi martani kan zagin Annabi da wata mata ta yi

Yanzun nan: Shugaban karamar hukumar Keffi da aka sace ya samu yanci
Yanzun nan: Shugaban karamar hukumar Keffi da aka sace ya samu yanci Hoto: The Nation
Asali: UGC

Kakakin yan sanda ya ce sun samu yancinsu da misalin karfe 9:00 na daren ranar Asabar kuma an sada su da iyayensu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, kakakin yan sandan ya ce an kama mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin a garin Gittata da ke karamar hukumar Keffi, Premium Times ta rahoto.

Ya kara da cewa:

“An kama wadanda ake zargin, wadanda suka zo daga jihar Kaduna yayin da suke tattauna kudin fansar da za a biya.”

Mista Nansel, ya kuma bayyana cewa yan sanda basu da masaniya kan ko an biya kudin fansa kafin sakin nasu.

Ya yi bayanin cewa yan bindigar sun saki mutanen ne saboda matsa lamba da suka samu daga hukumomin tsaro.

A halin da ake ciki, tuni aka binne jami’in dan sandan da aka kashe daidai da koyarwar addinin musulunci a Keffi, rahoton Guardian.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma da hadiminsa

A baya, mun kawo cewa miyagun yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa, Honorabul Muhammad Baba Shehu, da kuma direbansa.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa yan bindigan sun halaka dakaren ɗan sanda da ke tsare Ciyaman din, Sajan Alhassan Habibu Nasir.

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar Jumu'a a yankin Gudi, ƙaramar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel