EFCC ta gurfanar da Dasuki, Yuguda da Bafarwa gaban ƙuliya manta sabo

EFCC ta gurfanar da Dasuki, Yuguda da Bafarwa gaban ƙuliya manta sabo

Hukumar yaki zamba da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gurfanar da mai baiwa tsohon shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro kanal Sambo Dasuki tare da tsohon gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa da wasu mutane hudu gaban kotu kan zarginsu da hada kai wajen karkatar da kudi naira biliyan 19.

EFCC ta gurfanar da Dasuki, Yuguda da Bafarwa gaban ƙuliya manta sabo
Dasuki

EFCC ta gurfanar da Dasuki, da Bafarawa ne gaban babban kotun tarayya dake Abuja tare tsohon ministan kudi Bashir Yuguda, tsohon daraktan kudi na ofishin Dasuki, Shuaibu Salisu tare da ɗan Bafarawa da kuma kamfanin Bafarawa mai suna Dalhatu Ivestment Limited.

KU KARANTA: Hukumar yaki da fasa-kauri ta gano sabon salon shigo da motoci (HOTUNA)

EFCC na tuhumar wadanda ake zargin ne da laifuka 22 da suka danganci karkatar da makudan kudade kimanin naira biliyan goma sha tara (N19bn) mallakan gwamnatin tarayya wadanda aka diba daga asusun ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan lamurran tsaro Sambo Dasuki, da kua asusun rarraba kudaden kasa.

EFCC ta gurfanar da Dasuki, Yuguda da Bafarwa gaban ƙuliya manta sabo
Bafarawa

Sai dai dukkanin wadanda ake zargin sun musanta zargin, sa’annan lauyan su ya bukaci alkalin kotun, alkali Peter Affen daya bada belin wadanda yake karewa. Amma lauyan gwamnati Rotimi Jacobs ya nuna rashin amicewa da bukatar bada belinsa, inda yace tunda dai ba’a taba baiwa Dasuki beli ba, tare da ganin cewa yana hannun hukumar DSS, don haka ya baiwa alkalin shawara da kada ya wahalar da kansa.

Amma lauyan Dasuki ya shaida ma kotu, duk da cewa hukumar DSS taki sakin Dasuki, duk kuwa da cewar kotuna daban daban sun bada umarnin yin hakan, wannan ba shine zai zama uzurin hana Sambo Dasukin sabon belin ba.

daga karshe bayan alkali ya saurari dukkanin bagarorin guda biyu, sai ya daga cigaba da sauraron zuwa ranar 24 ga watan Feburairu.

Ku na iya samun mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel