Ziyara gidan Sarkin Kano: Buhari ya gana da iyalan wadanda bam ya tashi dasu a Kano

Ziyara gidan Sarkin Kano: Buhari ya gana da iyalan wadanda bam ya tashi dasu a Kano

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da 'yan uwan mutanen da harin bam ya rutsa dasu a jihar Kano
  • A yau ne shugaban kasar ya kai ziyara Kano, inda ya gana da Sarkin Kano a fadarsa jim kadan bayan
  • A makon da ya gabata ne aka samu fashewar bam a unguwar sabon gari da ke jihar, laamrin da ya tada hankali

Jihar Kano - This Day ta rahoto cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan uwan wadanda suka mutu sakamakon fashewar nakiya da ya faru a Kano.

Shugaban wanda ya ziyarci Kano domin halartar taron makon sojojin saman Najeriya, ya gana da ‘yan uwan mutum 9 da suka rasu a fadar Sarkin Kano, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Makon sojojin sama: Bayan tashin nakiya, Shugaba Buhari ya kai wata ziyara Kano

Buhari ya jajanta wa iyalan da Sarki da gwamnatin jihar Kano kan wannan mummunan lamari, wanda ‘yan sanda suka ce fashewar iskar gas da wani sinadarai ne amma daga baya suka sauya batu.

Buhari ya dura Kano, ya gana da 'yan uwan wadanda suka mutu sanadiyyar bam
Yanzu-Yanzu: Buhari ya gana da iyalan wadanda bam ya tashi dasu a Kano | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake jawabi tun da farko, gwamnan na Kano ya ce gwamnati ta bayar da Naira miliyan 9 a matsayin diyya ga iyalan wadanda suka rasu yayin da aka ba mutane 10 da suka samu munanan raunuka Naira miliyan 2.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika an ba da Naira miliyan daya ga wadanda suka samu kananan raunuka su raba.

Gwamnan ya kuma ce wata cibiyar kasuwanci mai suna African Centre da fashewar ta shafa an ba su Naira miliyan 2 yayin da kuma Winners Academy da dalibanta suka samu raunuka sakamakon fashewar gilashi ta samu Naira miliyan daya.

A nasa bangaren, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gode wa shugaban kasar bisa wannan karimcin da ya nuna, inda ya ce jama’ar Kano ba su yi mamakin ziyarar shugaban ba, domin kuwa shi (Buhari) ya kasance na talakawa.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya bayyana irin yadda yake matukar son gaje Buhari, ya ce ba wasa yake ba

Ya yi addu’ar Allah ya sa shugabanni masu gaskiya su fito a Najeriya a lokacin da babban zabe mai zuwa ya ke tunkarowa.

Makon sojojin sama: Bayan tashin nakiya, Shugaba Buhari ya kai wata ziyara Kano

A wani labarin, an dasa jami’an tsaro sosai a wasu muhimman wurare a cikin birnin Kano a shirye-shiryen isar shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar.

Ana sa ran shugaban kasar zai kaddamar da taron makon sojojin saman Najeriya a Kano.

Daily Trust ruwaito cewa, ta lura an mamaye titin da ke zuwa fadar Sarkin Kano tare da jibge jami’an tsaro rike da makamai a kan titin da motocinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel