Makon sojojin sama: Bayan tashin nakiya, Shugaba Buhari ya kai wata ziyara Kano

Makon sojojin sama: Bayan tashin nakiya, Shugaba Buhari ya kai wata ziyara Kano

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a jihar Kano domin halartar wani taron sojojin saman Najeriya
  • Zuwan shugaban Kano na zuwa ne kwanaki kadan bayan tashin wata nakiya a unguwar Sabon Gari da birnin
  • Rahotanni sun bayyana cewa, tuni aka jibge jami'an tsaro a yankunan da shugaban kasar zai kai ziyarar

Jihar Kano - An dasa jami’an tsaro sosai a wasu muhimman wurare a cikin birnin Kano a shirye-shiryen isar shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar.

Ana sa ran shugaban kasar zai kaddamar da taron makon sojojin saman Najeriya a Kano.

Daily Trust ruwaito cewa, ta lura an mamaye titin da ke zuwa fadar Sarkin Kano tare da jibge jami’an tsaro rike da makamai a kan titin da motocinsu.

Kara karanta wannan

An shiga rudani, wasu sun 'sace' masu kada kuri’a wajen zaben tsaida ‘Yan takaran PDP

Buhari zai kai ziyara jihar Kano
Makon sojin sama: Bayan tashin nakiya, Shugaba Buhari zai kai ziyarar aiki Kano | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

A fadar sarkin, an ga daruruwan jami’an tsaro dauke da makamai da suka hada da jami’an ‘yan sandan Najeriya, jami’an tsaro na farin kaya, sojojin Najeriya, da sauransu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai an hana ‘yan jarida shiga fadar, inda ake sa ran shugaban zai ziyarta kafin ya nufi wurin taron makon rundunar ta sojojin sama.

An ruwaito cewa, a makon da ya gabata an samu fashewar nakiya a unguwar Sabongari da ke jihar Kano wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara tare da jikkata wasu da dama.

Kwanaki biyu bayan fashewar nakiyar, rundunar ‘yan sandan ta ce ta gano wata mota makare da kayan makamai, bindigu da alburusai.

Buhari ya sauka a jihar Kano

Jim kadan bayan rahoton da muka samo daga Daily Trust, fadar shugaban kasa ta tabbatar da tafiyar shugaban jihar Kano.

Kara karanta wannan

Ka zabi Ganduje matsayin mataimakin shugaban kasa, an yi kira ga Tinubu

A wani bidiyon da wakilin Legit.ng Hausa ya samo daga shafin Facebook na hadimin Buhari, Bashir Ahmad, an ga lokacin da shugaban ya sauka a jirgi.

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

A wani labarin, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

Asali: Legit.ng

Online view pixel