Rudani: 'Yan bindiga sun sako hakimin kauyen Kano, sun rike farfesan da ya kai kudin fansa

Rudani: 'Yan bindiga sun sako hakimin kauyen Kano, sun rike farfesan da ya kai kudin fansa

  • Basaraken gargajiyan da aka sace a jihar Kano ya samu 'yanci bayan da aka kai kudin fansa ga 'yan bindiga
  • Sai dai, an samu tsaiko yayin da 'yan bindigan suka ajiye farfesan da ya kai kudin fansa saboda wani dalili
  • Rahotanni da suke fitowa daga dangi sun bayyana sako basaraken, kana da ajiye farfesan a maboyar 'yan bindiga

Jihar Kano - Daily Trust ta rahoto cewa, hakimin Karfi da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano, Abdulyahyah Ilo da aka sace ya samu ‘yanci daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

Masu garkuwan, sun rike karamin farfesa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (KSTU), Wudil, Huzaifa Karfi, wanda rahotanni suka ce ya je ne domin kai kudin fansa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun kashe 3 a dangin shugaban karamar hukuma da mai gadi

Rahoton The Guardian ya ruwaito cewa ‘yan bindigan sun kashe mutane shida da suka yi kokarin ceto basaraken kauyen a lokacin da suka yi awon gaba da shi.

'Yan bindiga sun sako sarkin da suka sace, sun rike wanda ya kawo kudin fansa
Rudani: 'Yan bindiga sun sako hakimin kauyen Kano, sun rike farfesan da ya kai kudin fansa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

An ce sun mamaye kauyen ne a kan babura uku daga jihar Bauchi ta dajin Ringim da ke Jigawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mazaunin yankin mai suna Musa Sa’ad ya tabbatar da sakin basaraken da masu garkuwa da mutane suka yi.

Ya bayyana cewa mafarauta da ’yan banga sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a cikin daji da ke da nasaba da sace-sace a kauyen Karfi.

A cewar majiya:

“Sun karbi kudin fansa tare da tsare Dr Huzaifa saboda da mutumin da ‘yan banga suka kama. Sun bukaci a sako mutumin nasu a matsayin sharadin sakinsa.”

Wani dan uwa ga sarkin gargajiyan, Yusuf Ismail ya tabbatar da cewa an sako basaraken kuma yana jinya a asibiti.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, bai iya tabbatar da faruwar lamarin ba, amma ya yi alkawarin ba da bayani idan ya samu.

Masu Garkuwa Sun Sake Kashe Wani Ɗan Kasuwan Kano Bayan An Biya Kuɗin Fansarsa

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ka hanyar Kaduna-Birnin Gwari sun sake kashe wani dan kasuwan Kano, Umar Sani, bayan karbar kudin fansa daga yan uwansa, rahoton Daily Trust.

An sace dan kasuwan wanda ake kira Magaji ne kimanin makonni biyu tare da wasu mutane biyar a hanyarsu ta zuwa Buruku amma daga baya wadanda suka sace shi suka kashe shi bayan karbar kudin fansarsa.

Marigayin dan asalin karamar hukumar Fagge ne a birnin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel