Da duminsa: 'Yan sanda sun yi ram da miyagun da suka yi garkuwa da daliban jami'ar Greenfield

Da duminsa: 'Yan sanda sun yi ram da miyagun da suka yi garkuwa da daliban jami'ar Greenfield

  • Rundunar'yan sandan Najeriya sun yi ram da wasu biyu, Aminu Lawal da Murtala Dawu da ake zarginsu da hannu wajen garkuwa da daliban jami'ar Greenfield
  • Daga cikin laifukan da ake tuhumarsu sun hada da halaka biyar daga cikin daliban jami'ar tare da mai gadinsu kafin biyan kudin fansa, daga bisani suka saki sauran
  • Binciken sirri na nuna yadda suke cin karensu babu babbaka a yankin Dan Hunu, Kekebu, Dan Busha Rido, Maraban Rido, da Kumi Sata duk a jihar Kaduna

Kaduna - Rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF) ta ce ta kama wasu mutum biyu - Aminu Lawal da Murtala Dawu - da ake zarginsu da hannu wajen garkuwa da daliban jami'ar Greenfield dake Kaduna.

Vanguard ta ruwaito cewa, a ranar 20 ga watan Afirilu 2021, 'yan bindiga dauke da makamai sun shiga makarantar, inda su ka yi awon gaba da dalibai 20 da malamai uku na jami'ar.

Kara karanta wannan

Kaduna: Rayuka 3 sun salwanta, miyagu sun sace mutum 9 a sabon farmaki

Da duminsa: 'Yan sanda sun yi ram da miyagun da suka yi garkuwa da daliban jami'ar Greenfield
Da duminsa: 'Yan sanda sun yi ram da miyagun da suka yi garkuwa da daliban jami'ar Greenfield. Htot daga dailytrust.com
Asali: UGC

An halaka biyar daga cikin daliban da mai gadinsu namiji a yayin da suke hannun masu garkuwa da mutanen.

A ranar 29 ga watan Mayu, 2021, hukumar makarantar ta bayyana yadda 'yan bindiga suka saki jerin sunaye na karshe na sauran daliban da malamai marasa koyarwan da suka yi garkuwa da su, bayan an biya kudin fansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TheCable ta ruwaito cewa, yayin jawabi kan wadanda ake zargin, Muyiwa Adejobi, kakakin 'yan sanda, ya ce biyun Lawal da Dawu sun fallasa yadda suka halaka biyar daga cikin daliban jami'ar Greenfield.

"Manya daga cikin abubuwan da ake tuhumarsu sun hada da laifin garkuwa da mutane inda biyun Aminu Lawal (wanda aka fi sa ni da Kano), da Murtala Dawu (Mugala), wadanda ke hada kai da tawagar masu garkuwa da mutane wacce aka fi sa ni da Ashana, suka fallasa ta'addancin da su ka yi sannan suka halaka 'yan sanda biyu da 'dan sa kai daya a shekarar 2021," a cewar Adejobi.

Kara karanta wannan

Rashawar N80bn: EFCC ta sauya wa Akanta-Janar wurin zama daga Kano inda aka kama shi

"Haka zalika, sun fallasa yadda su ka yi garkuwa da daliban jami'ar Greenfield ta jihar Kaduna, sanan ba tare da tausayi ba suka halaka biyar daga cikin wadanda su ka yi garkuwa da su kafin a biya kudin fansa, daga bisani suka saki sauran.
"Binciken sirri ya bayyana wuraren da suke cin karensu babu babbaka wanda ya hada da; Dan Hunu, Kekebu, Dan Busha Rido, Maraban Rido da Kumi Sata, duk a jihar Kaduna.
"Jami'an FIB-STS sun yi ram da su a watan Maris 2022, baya ga tuhumarsu da ake da sa hannu wajen yin garkuwa da daliban Bethel Baptist a shekarar 2021," ya kara da cewa.

El-Rufai: Cigaba da ruwan bama-bamai a dajika zai magance ta'addanci

A wani labari na daban, akwai bukatar cigaba da ayyukan sojoji tare da ruwan bama-bamai a dajikan yankunan arewa maso yamma da jihar Niger, Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce a jiya.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

Ya yarda cewa wannan ayyukan za su kawo tsaro a jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Filato da Niger kuma za su kawo karshen ta'addanci.

The Nation ta ruwaito, Gwamnan ya sanar da hakan ne a Zaria yayin shagalin bikin gargajiya na Hawan Bariki wanda Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli yayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng