El-Rufai: Cigaba da ruwan bama-bamai a dajika zai magance ta'addanci

El-Rufai: Cigaba da ruwan bama-bamai a dajika zai magance ta'addanci

  • Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce cigaba da ruwan bama-bamai a dajika zai kawo karshen ta'addanci
  • Ya bayyana cewa, akwai masu kai wa 'yan ta'adda bayanai, su ne ke kara rura wutar ta'addanci a arewa maso yamma
  • Gwamnan ya sanar da cewa akwai bukatar hadin kai da masarautun gargajiya wurin magance matsalar tsaro

Zaria, Kaduna - Akwai bukatar cigaba da ayyukan sojoji tare da ruwan bama-bamai a dajikan yankunan arewa maso yamma da jihar Niger, Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce a jiya.

Ya yarda cewa wannan ayyukan za su kawo tsaro a jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Filato da Niger kuma za su kawo karshen ta'addanci.

El-Rufai: Cigaba da ruwan bama-bamai a dajika zai magance ta'addanci
El-Rufai: Cigaba da ruwan bama-bamai a dajika zai magance ta'addanci. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

The Nation ta ruwaito, Gwamnan ya sanar da hakan ne a Zaria yayin shagalin bikin gargajiya na Hawan Bariki wanda Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli yayi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

El-Rufai ya ce masu kai wa 'yan ta'adda bayanai su ke taimakawa wurin tabbatar da ta'addanci.

Gwamnan ya ce: "Aikina na farko a matsayin gwamna shi ne kiran taron gaggawa na tsaro a ranar 30 ga watan Mayun 2015 domin gano kalubalen tsaro a fadin jihar kuma mu samo amsoshin su.
"Daya daga cikin abinda muka samu a taron shi ne hukuncin hada kai da gwamnonin jihohin arewa maso yamma da Niger wurin daukar nauyin ayyukan sojoji domin kakkabe dajin Kamuku zuwa Kuyambana a yankin Birnin Gwari inda ake boye shanun sata."

Kano: Ganduje ya haramta zuwa da fostoci masallatan idi ko wurin shagulgulan sallah

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya haramta yawo da manyan fostoci da kanana yayin sallar Idi da sauran shagulgulan sallah, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

A sakon sallanshi da kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar a wata takarda, gwamnan ya ce hakan zai iya kawar da hankali daga sallah.

"Yayin da ake ganinsu bauta mai matukar muhimmanci bayan tsawon lokacin da aka dauka ana azumin Ramadana, inda shagulgulan al'adu ke biyo baya."
"Saboda haka, baya kyautuwa ga mutum ko jam'iyyar siyasa su rage wa wurin bautar kima ta hanyar amfani da kayayyakin kamfen," a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel