Yajin ASUU: Tashin hankali yayin da sojoji ke harba bindigogi a wurin zanga-zangar dalibai

Yajin ASUU: Tashin hankali yayin da sojoji ke harba bindigogi a wurin zanga-zangar dalibai

  • Daliban jami'a sun fito zanga-zanga a jihar Ondo, sun gamu da sojoji yayin da suke tsaka da gudanar da zanga-zangar lumana
  • Wannan lamari na zuwa ne yayin da daliban ke gudanar da zanga-zanga na kwanaki biyu a yankin Kudu maso Yamma
  • Zanga-zangar na zuwa ne lokacin da jami'o'in Najeriya ke rufe saboda tsananin yaji da malaman jami'a suka shiga

Jihar Ondo - Ana zargin cewa wasu jami’an sojin Najeriya sun kai farmaki wurin da dalibai ke gudanar da zanga-zanga a garin Akure na jihar Ondo a ranar Talata.

Daliban sun fita zanga-zangar kwana biyu a jihar ne saboda yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta shiga.

Bidiyon da Punch tace ta samo ya nuna yadda tarin sojoji ke tafiya dauke da bindigogi, tare da mota da ke bin su a baya. An ji karar harbe-harbe a lokacin da suke tafiya yayin da wasu daga cikin daliban suka ruga da gudu cikin firgici.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An fara harbe-harben bindiga a wurin da 'Tukunyar Gas' ta fashe a Kano

Yajin aikin ASUU ya kai ga zanga-zangar dalibai
Yajin ASUU: Tashin hankali yayin da sojoji ke harba bindigogi a wurin zanga-zangar dalibai | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Daliban Jami’ar Adekunle Ajasin ta Akungba da ke Akure, tare da takwarorinsu na jihohi makwabta, sun mamaye manyan tituna da suka hada da hanyar Benin zuwa Ore a yayin da suke zanga-zangar, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyoyi sun shaida cewa, tun a jiya ‘yan sanda da sojoji suka zo wurin zanga-zangar, amma a yau sun zo da nufin tashin hankali inda suka fara tarwatsa daliban tare da hargitsa wasu abubuwa.

A bayanin wani ganau:

"Abin da ya faru a Lekki yana son sake faruwa a Ondo!" daya daga cikin masu zanga-zangar ya yi kururuwa a wani faifan bidiyo da ke nuna zanga-zangar bata tafi daidai ba.

Wani kuwa na cewa: "Kashe mu suke."

An ruwaito cewa a makon da ya gabata, a Ibadan, wasu sojojin Najeriya sun yi yunkurin bindige daliban da suka fito zanga-zanga a kusa da jami'ar Ibadan. An yi Allah wadai da hakan a wata sanarwa da kungiyar ASUU ta jihar Legas ta fitar.

Kara karanta wannan

Matasa sun nuna fushinsu yayin da wata Naomi Goni ta kara ɓatanci ga Annabi SAW, an kama 3

Sama da mako guda dalibai ke gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya kan yajin aikin ASUU, suna masu kira ga gwamnatin tarayya da ta amince da bukatun malaman da suke yajin aikin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, yajin aikin ASUU da ya fara a ranar 14 ga watan Fabrairu ya shiga kwanaki 92.

An saki sakamakon jarabawar JAMB a Najeriya

A wani labarin, hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'in Najeriya watau JAMB ta sanar da sakin sakamakon jarabawar bana 2022 da dalibai a fadin tarayya suka zana.

Shugaban sashen hulda da jama'a na JAMB, Fabian Benjamin, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, rahoton TheNation.

Ya bayyanawa dalibai da suka zana jarabawar cewa za su iya duba sakamakonsu a wayoyinsu na tarho. A cewarsa, su tura sakon akwatin SMS 'UTMERESULT zuwa 55019 a wayar da aka musu amfani wajen rijista.

Asali: Legit.ng

Online view pixel