Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun bayyana sunayen kananan hukumomi 9 da zasu kai hari

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun bayyana sunayen kananan hukumomi 9 da zasu kai hari

  • Miyagun yan bindiga sun aike da wasika ɗauke da jerin sunayen wasu kananan hukumomi 9 da zasu kai hari nan ba da jimawa ba
  • Hakan ya zo ne awanni bayan wasu mahara sun farmaki karamar hukuma da Kotu, inda suka aikata ɓarna mai yawa duk a Anambra
  • A wasikar yan bindigan sun gargaɗi gwamnan Anambra da jami'an tsaro su shirya tarban su don gwabzawa

Anambra - Yan bindiga sun rubuta wasika zuwa kananan hukumomi 9 da zasu kai wa farmaki nan ba da jimawa ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sunayen ƙananan hukumomin da suka ayyana kai hari sun haɗa da, Ihiala, Aguata, Nnewi ta kudu, Awka ta arewa, Awka ta kudu, Idemili ta arewa, Idemili ta kudu, Orumba ta kudu, Orumba ta arewa da Anambra ta gabas.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Iyaye sun fara tururuwar kwashe 'ya'yan su bayan abu ya Fashe da ɗalibai a Kano

Rashin tsaro a Anambra.
Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun bayyana sunayen kananan hukumomi 9 da zasu kai hari Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A sakon da suka turaw kowace karamar hukuma daga ciki, kungiyar yan bindigan da bata bayyana sunanta ba ta gargaɗi jami'an tsaro su shirya gwabzawa a "ƙasar Biafara."

Sun rubuta a wasikar cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Waɗan nan kananan hukumomin su jira zuwan mu nan ba da jimawa ba, muna gargaɗin Farfesan mu wannan lokacin aiki ne ba na magana da fatar baki ba. Duk jami'an tsaron da ke wuraren su shirya."
"Ka je ka faɗa wa shugaban ƙasa ya saki Ogan mu, Mazi Nnamdi Kanu ko kuma a cigaba da yaƙi. Gargaɗi na ƙarshe."

Yan sanda sun kashe masu tilasta zaman gida a Anambra

A ranar Talata, dakarun yan sanda na jihar Anambra suka halaka yan bindigan da ke tilasta wa mutane zaman gida a sassan jihar.

Yan ta'addan sun addabi mutane a yankin Ogidi a rana ta biyu ta zaman gida da suke tilasta mutane, amma jami'an yan sanda suka yi ajalinsu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sokoto: An ayyana neman wadanda aka gani a bidiyon kone dalibar da ta zagi Annabi

Kakakin yan sanda na jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, yace hukumar yan snada ta sauran hukumomin tsari na cigaba da aikin sintiri don tabbatarda bin doka da oda.

A wani labarin kuma An fara harbe-harben bindiga a wurin da 'Tukunyar Gas' ta fashe a Kano

Ƙarar harbe-harben bindiga ya tashi sosai a a wurin da tukunyar Gas ta fashe a yankin Sabon Gari, jihar Kano ranar Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro ne suka saki harbin domin tarwatsa dandazom mutanen da suka mamaye wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel