Kaduna: Wata budurwa ta maka mahifinta a Kotun kan ya ƙi aurar da ita

Kaduna: Wata budurwa ta maka mahifinta a Kotun kan ya ƙi aurar da ita

  • Wata budurwa ta kai ƙarar mahaifinta gaban Kotun musulunci kan ya ƙi yarda ya ɗaura mata aure da zaɓin zuciyarta
  • Yarinyar mai suna Halima ta shaida wa Kotu cewa zuciyarta ta kamu da soyayyar wani Bashir Yusuf, amma an ƙi musu aure
  • Mahaifin ya shaida wa Kotu abinda ya sa ya ƙi ɗaura mata aure da shi da yadda suka yi da mahaifin saurayin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Wata budurwa, Halima Yunusa, ta kai mahaifinta ƙara gaban Kotun Shari'ar Musulunci da ke zama a Magajin Gari, jihar Kaduna, bisa zargin mahaifin ya hana ta auren wanda take so, Bashir Yusuf.

Daily Trust ta rahoto cewa Halima wacce ke zaune a Kasuwan Magani, ƙaramar hukumar Chikun, ta faɗa wa Kotu cewa ta faɗa kogin soyayya da Yusuf amma iyayenta sun ki ɗaura musu aure.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ministan albarkatun man fetur ya janye daga takarar shugaban kasa a 2023

Mahaifin Halima, Ibrahim yayin da yake kare kansa, ya ce ya san tsananin soyayyar da ke tsakanin diyarsa da kuma Yusuf. Sai dai Yusuf ya gaza bin matakan aure.

Kotun Musulunci a Kaduna.
Kaduna: Wata budurwa ta maka mahifinta a Kotun kan ya ƙi aurar da ita Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A jawabinsa mahaifin Halima ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ya zo wurina ya nuna mun yana da sha'awar auren ɗiyata. Na faɗa masa ya je ya zo da iyayensa ko wasu daga cikin magabatansa, har yau be dawo ba shekara ɗaya kenan."
"Bayan tsawon lokaci kusan shekara sai ya dawo ya ɗauki ɗiyata suka gudu na tsawon kwana uku. Mun samu labarin sun dawo sun je gidan yar uwata. Muka faɗa wa yan sanda suka kama su aka hukunta su."

Dalilin rashin ɗaura musu aure

Bayan fitowarsu daga hannun yan sanda, Ibrahim ya faɗa wa Kotu cewa sun sake guduwa zuwa Abuja na tsawon mako biyu.

Kara karanta wannan

Sokoto: Wani Malami ya yi alkawarin daukar nauyin iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi, yace sun gama wahala a duniya

"Daga ƙarshe muka haɗu da uban saurayin muka tattauna kan lamarin. ya faɗa mun ba zai taɓa barin ɗansa ya auri ɗiyata ba."
"Wasa-wasa sai da muka je gaban magajin garin kauyen mu aka rubuta a takarda muka sanya hannu har da shaidu kan cewa zan gargaɗi ɗiyata ta rabu da saurayin."

A ɓangarensa, Saurayin da ake ta mahawara kan shi, Yusuf, ya bayyana cewa yana matuƙar kaunar Halima.

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Mai Shari'a Murtala Nasir, bayan sauraron kowane ɓangare ya yanke cewa ya kamata a jawo hankalin mahaifin Yusuf ya bar yaran su auri junansu.

"Idan ya ƙi ɗaukar shawara, zamu ɗaura musu aure a Kotu ko da kuwa ba zai sa musu albarka ba," inji Alƙalin.

Ya shawarci Halima ta nemi afuwar iyaye da yan uwanta domin ta samu albarkar su a rayuwarta nan gaba.

Ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Mayu, 2022 domin mahaifin Yusuf ya halarci kotun a kawo ƙarshen lamarin.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Yan bindiga sun banka wuta a Kamfanin rarraba wutar lantarki, sun tafka ɓarna

A wani labarin na daban kuma Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Siyasar Kano ta ƙara rikicewa musamman tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Bayan ziyarar Ganduje gidan Shekarau don hana shi komawa NNPP, Kwankwaso ya tura tawaga kafin zuwansa gidan Shekarau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel