Samun wuri: Tsagerun 'yan bindiga sun kirgo kananan hukumomi 9 da za su addaba a Anambra

Samun wuri: Tsagerun 'yan bindiga sun kirgo kananan hukumomi 9 da za su addaba a Anambra

  • Rahotanni sun kawo cewa tsagerun yan bindiga na shirin kai farmaki wasu kananan hukumomi guda tara a jihar Anambra
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da maharan suka aika jihar, sun kuma bukaci jami'an tsaro da su zama cikin shiri
  • Yankunan da za a kaiwa harin sune Ihiala, Aguata, Nnewi South, Awka North, Awka South, Idemili North, Idemili South, Orumba South, Orumba North da Anambra East

Anambra - Wasu da ake zaton yan bindiga ne sun lissafa kananan hukumomi tara a jihar Anambra wanda za su kaiwa hari kwanan nan, jaridar The Nation ta rahoto.

Ci gaban na zuwa ne bayan jami’an tsaro sun kashe mutane hudu da ke tabbatar da dokar zaman gida a ranar Talata a Ogidi, karamar hukumar Idemili North.

Kara karanta wannan

Sokoto: An ayyana neman wadanda aka gani a bidiyon kone dalibar da ta zagi Annabi

Kananan hukumomin da aka lissafa don kaiwa harin sune: Ihiala, Aguata, Nnewi South, Awka North, Awka South, Idemili North, Idemili South, Orumba South, Orumba North da Anambra East.

Samun wuri: Tsagerun 'yan bindiga sun kirgo kananan hukumomi 9 da za su addaba a Anambra
Samun wuri: Tsagerun 'yan bindiga sun kirgo kananan hukumomi 9 da za su addaba a Anambra Hoto: Punch
Asali: UGC

Sun aika da sakon ne a karshen mako ta hannun wani direba, suna masu gargadin jami’an tsaro da su shirya ma aiki a kasar Biyafara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar takardar da suka aiko:

“Wadannan kananan hukumomi su jira mu nan ba da dadewa ba.
“Muna gargadin farfesanmu cewa lokaci ya yi da za a dauki mataki ne ba wai lokacin fadin manyan zantuka da maganganu ba.
“Dukkanin jami’an tsaro da suka mamaye kasar Biyafara su shirya ma aiki.
“Ku je ku fadama shugaban kasar Zoo ya saki shugabanmu Onyendu, Mazi Nnamdi Kanu ko ya fuskanci yaki mara karewa-gargadi na karshe.”

Jami’an tsaro a ranar Talata sun gano yan iskar da suka kai hari a Ogidi sannan suka yi waje da su.

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

An tattaro cewa wadanda ake zargin su hudu suna ta tursasa dokar zaman gida a yankin Ogidi lokacin da jami’an tsaro suka far masu.

Kakakin yan sandan Anambra, Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridarPunch ta rahoto.

Ya ce rundunar da sauran hukumomi masu alaka suna ta fatrol domin tabbatar da doka da oda a jihar.

Tochukwu ya ce a bari mutane su dunga gudanar da harkokinsu ba tare da tsoratarwa da cin zarafi ba.

Karin bayani: An bindige tsagerun IPOB da ke addabar jama'a a jihar Anambra

A baya mun ji cewa an harbe wasu ‘yan bindiga biyu da ke tilasta dokar “zama-a-gida” da haramtacciyar kungiyar IPOB ke kakabawa jama'ar jihar Anambra.

A cewar rundunar ‘yan sanda, an kashe su ne a hanyar Umunze a karamar hukumar Orumba ta Kudu a Anambra ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce jami’an da ke sintiri kan hana aikata laifuka sun yi arangama da tsagerun dake addabar jama'ar jihar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: An bindige tsagerun IPOB da ke addabar jama'a a jihar Anambra

Asali: Legit.ng

Online view pixel