Karin bayani: An bindige tsagerun IPOB da ke addabar jama'a a jihar Anambra

Karin bayani: An bindige tsagerun IPOB da ke addabar jama'a a jihar Anambra

  • 'Yan ta'addan IPOB sun gamu da ajalinsu yayin da jami'an tsaro suka far musu a lokacin da suke barna
  • Rahoto ya bayyana cewa, an samu wasu 'yan IPOB da ke tilastawa mazauna Anambra dokar zaman gida a yau Litinin
  • Hakan bai zo musu da sauki ba yayin da jami'an tsaro suka yi arangama dasu a wani yankin jihar

Jihar Anambra - An harbe wasu ‘yan bindiga biyu da ke tilasta dokar “zama-a-gida” da haramtacciyar kungiyar IPOB ke kakabawa jama'ar jihar Anambra.

A cewar rundunar ‘yan sanda, an kashe su ne a hanyar Umunze a karamar hukumar Orumba ta Kudu a Anambra ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Yadda aka bindige tsageru a Anambra
Da dumi-dumi: An bindige tsagerun IPOB da ke addabar jama'a a jihar Anambra | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce jami’an da ke sintiri kan hana aikata laifuka sun yi arangama da tsagerun dake addabar jama'ar jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ministan albarkatun man fetur ya janye daga takarar shugaban kasa a 2023

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra da ke sintiri a safiyar yau 16/5/2022 a kan hanyar Umunze, kan titin karamar hukumar Orumba ta Kudu, sun kama ‘yan bindiga dauke da muggan makamai da ake zargin suna tilasta haramtacciyar dokar zama a gida a jihar Anambra.”
“Jami’an tsaro sun kashe biyu daga cikin tsagerun tare da kwato wata farar mota Toyota Hiace Bas. Karin bayani sun nuna cewa wadannan bata-gari na kawo cikas ga zirga-zirgar masu amfani da hanyar da ba su ji ba ba su gani ba da ke zuwa kasuwancinsu.
"Y'an ta’addan da karfin tsiya suna karbar babura da keke napep, suna korar fasinjoji, kuma su baburan ko keke napep din.”

Sai dai ya ce jami’an ‘yan sandan sun zafafa sintiri a jihar kuma ana sa ido kan lamarin, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Yan bindiga sun banka wuta a Kamfanin rarraba wutar lantarki, sun tafka ɓarna

Rikici yayin da jami'in gidan yari ya bindige dan kasuwa akan karan taba sigari a Kano

A wani labarin, wani jami'in gidan yari dauke da makami da ke aiki da gidan yarin Goron Dutse a jihar Kano ya tafka kuskure, inda ya harbe wani dan kasuwa har lahira bayan wata zazzafar musayar yawu.

Jami'in gidan yarin mai suna Adamu, ana zargin ya harbe dan kasuwar ne bayan wata takadama tsakaninsa da dan kasuwan kan taba sigari.

An tabbatar da mutuwar dan kasuwar a lokacin da aka kai shi asibiti, inji rahoton Sahelian Times.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.