Shirin 2023: Tsoffin gwamnonin Jigawa sun gama kai a PDP, domin kassara APC a jihar

Shirin 2023: Tsoffin gwamnonin Jigawa sun gama kai a PDP, domin kassara APC a jihar

  • Jiga-jigan PDP a jihar Jigawa sun hada kai domin kawo karshen mulkin APC, inda tsoffin gwamnoni biyu suka hade a inuwa daya
  • Saminu Turaki ya koma jam'iyyar PDP, inda ake kyautata zaton zai tsaya takarar sanata a mazabarsa
  • Saminu Turaki dai yana daya cikin jigogin jihar kuma shi ya fara mulkar jihar tun dawowar mulkin farar hula

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Jigawa - A ranar Litinin ne tsohon gwamnan jihar Jigawa, Saminu Turaki, ya koma jam’iyyar PDP inda ya kawo karshen zamansa a jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan.

Turaki ya koma PDP ne tare da jiga-jigan ‘yan siyasa na jam’iyyar APC na gundumarsa ciki har da tsohuwar kwamishiniyar harkokin mata a jihar, Ladi Dansure.

Tsohon gwamnan ya shaidawa manema labarai a gidansa na Kano cewa ya koma jam’iyyar PDP ne domin ciyar da jihar Jigawa gaba da kuma ‘yantar da jama’a daga mulkin kama-karya na 'yan APC.

Kara karanta wannan

Wani dan takarar shugaban kasa ya karaya ya kai karar PDP kan kudin fom N40m

Turaki ya koma PDP domin lallasa APC
Shirin 2023: Tsoffin gwamnonin Jigawa sun gama kai a PDP, domin kassara APC a jihar | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A kalamansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A matsayina na shugaba ban koma PDP don samun wani matsayi ba amma, zan yi iya kokarina na jagoranci jam'iyyar zuwa ga nasara a zaben 2023 mai zuwa."

Turaki zai tsaya takarar sanata

Sai dai jaridar Premium Times ta ce ta samu labarin cewa Turaki ya fito takarar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Yamma.

An ce wani dan takarar kujerar a karkashin jam’iyyar PDP, Nasiru Roni ya janye masa, kamar yadda majiya ta shaida.

A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Babandi Gumel, ya ce tsohon gwamnan ya koma PDP tare da dubban magoya bayansa.

Ya ce Turaki ya samu tarba daga dukkan iyalan PDP a Jigawa ciki har da tsohon gwamna Sule Lamido, haka nan Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban PDP ya tabbatar wa ‘yan jam’iyyar cewa jam'iyya za ta yi adalci ga dukkan mambobinta sabbi da tsoffi.

Kara karanta wannan

2023: Ganduje ya bayyana ainahin dalilin da yasa ya tsayar da Nasiru Gawuna don ya gaje sa

Turaki, wanda ya yi gwamnan jihar Jigawa na tsawon wa’adi biyu daga 1999 zuwa 2007, yana fuskantar tuhume-tuhume 32 na karkatar da Naira biliyan 36 a lokacin da yake kan mulki.

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

A wani labarin, bangarorin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara sun gudanar da gangami na musamman don tabbatar da dinke barakar da ake da ita.

Jaridar Daily Trust ta ce wannan gangami da aka shirya ya nuna an kawo karshen rikicin cikin gidan da aka dauki lokaci ana fama da shi a jam’iyyar.

An yi taron ne a filin wasan Ahmadu Bello da ke garin Gusau. Kusan duka manyan jagororin APC sun samu halartar wannan fitowa da aka yi a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel