Yanzu-yanzu: Ranar Litinin za'a dawo jigilar mutane a jirign kasan Abuja-Kaduna, Gwamnatin tarayya

Yanzu-yanzu: Ranar Litinin za'a dawo jigilar mutane a jirign kasan Abuja-Kaduna, Gwamnatin tarayya

Legas - Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ranar Litinin, 23 ga watan Mayu, 2022 za'a dawo jigilar fasinjoji a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

An dakatar da jigilar mutane ne sakamakon harin Bam da yan bindiga suka kaiwa jirgin a watan Maris.

An yi awon gaba da mutane kimanin 70.

Kakakin hukumar sufurin jiragen kasa NRC, Yakubu Mahmood, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar.

Yace hakan ba ya nurfin cewa ba za'a cigaba da kokarin ceto wadanda yan bindiga suka sace ba.

Iyalan wadanda aka sace sun yi barazanar cewa ba zasu taba amincewa jirgin ya dawo aiki ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Online view pixel